’Yan sanda za su hada kai da mutanen gari wajen kakkabe miyagu a Kano

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Malam Habu Ahmad Sani ya ce rundunarsu za ta inganta alakarta da mutanen gari wajen ganin an kakkabe aikata laifuffuka a fadin jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko a Kano. Habu Sani ya ce rundunar za ta yi aiki […]

’Yan sanda za su hada kai da mutanen gari wajen kakkabe miyagu a Kano
’Yan sanda za su hada kai da mutanen gari wajen kakkabe miyagu a Kano

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Malam Habu Ahmad Sani ya ce rundunarsu za ta inganta alakarta da mutanen gari wajen ganin an kakkabe aikata laifuffuka a fadin jihar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko a Kano.

Habu Sani ya ce rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin sa-kai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewarsa, rundunarsu za ta tabbatar da cewa, “Bangaren kyautata alaka tsakanin ’yan sanda da jama’ar gari zai kara kaimi wajen tabatar wa jama’a damar ganawa da mu kai-tsaye ta hanyoyi da muka tsara. Tuni muka umarci shugabbannin ofisoshin ’yan sanda da ke sassan jihar su tabbatar cewa a kowane mataki an kyautata wannan dangantaka domin samo hanyoyin magance matsalar tsaro a jihar nan.”

Kwamishinan ya gargadi masu aikata laifuffuka su tuba domin ’yan sanda ba za su zuba musu idanu ba.

Kwamishina Habu Sani ya kama aiki ne a matsayin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ne a ranar 20 ga Nuwamban nan inda ya gaji tsohon Kwamishina Ahmed Iliyasu wanda aka yi wa karin girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar na  ’Yan sandan Najeriya.