‘Yan sanda za su kwace makaman ‘yan Biyafara
Babban Sufeton ‘yan sandan ya buƙaci kwamishinonin ‘yan sandan jihohin yankin Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Kudancin kasar su ƙwace makaman da ke hannun ‘yan fafutukar kafa ƙasar Biyafra, kamar yadda BBC ta bayyana. Mista Solomon E. Arase, wanda ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda Olabisi Kolawole ta aikewa manema labarai, […]

Babban Sufeton ‘yan sandan ya buƙaci kwamishinonin ‘yan sandan jihohin yankin Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Kudancin kasar su ƙwace makaman da ke hannun ‘yan fafutukar kafa ƙasar Biyafra, kamar yadda BBC ta bayyana.
Mista Solomon E. Arase, wanda ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda Olabisi Kolawole ta aikewa manema labarai, ya ce matakin ya zama wajibi ganin yadda ‘yan Biyafara suka far ma ‘yan sandan da ke yunƙurin samar da zaman lafiya a yankin