’Yan sandan Adamawa sun harbe dan fashi tare da kama biyu

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun harbe dan fashi daya tare da kama biyu, bayan sun yi artabu da wata kungiyar ’yan fashi da suka addabi jama’ar jihar. An yi artabun ne da misalin karfe 9:30 na dare a ranar Litinin, a fafatawar da ’yan sandan suka yi da kungiyar ta ’yan fashi da ta […]

’Yan sandan Adamawa sun harbe dan fashi tare da kama biyu

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun harbe dan fashi daya tare da kama biyu, bayan sun yi artabu da wata kungiyar ’yan fashi da suka addabi jama’ar jihar.

An yi artabun ne da misalin karfe 9:30 na dare a ranar Litinin, a fafatawar da ’yan sandan suka yi da kungiyar ta ’yan fashi da ta addabi yankunan fadar jihar da suka kunshi unguwanni Dougirie da Karewa da Bekaji da kuma GRA.

A ranar Litinin din ’yan fashin sun shiga wasu gidaje a Layin Leki-Taba da ke Jimeta inda suka yi fashi a gidajen jama’a sannan suka doshi gidan wani Alhaji Sama’ila Bakari, inda wani da ya hango shigarsu ya yi maza ya aika sakon tes ga jami’an tsaro.

Sakamakon luguden wuta da aka yi a tsakanin ’yan sandan da ’yan fashin ne ya janyo mutuwar daya daga cikin ’yan fashin da harsashi ya tarwatsa kansa, aka kama sauran biyu, sannan uku suka tsere.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, Othman Abubakar ya ce sakon tes da aka aika musu ya taimaki ’yan sandan wajen isowa inda ake fashin da wuri sannan sakamakon harbe-harben, suka kashe dan fashi daya, sannan biyu suka mika wuya ga ’yan sanda.

 Othman ya ce makaman da aka samu daga ’yan fashin sun hada da karamar bindiga da harsasai shida da wayoyi hudu masu tsada sannan da gatari biyu.

 Abubakar yayi kira ga jama’ar jihar su ba da hadin kai wajen taimaka wa jami’an tsaro domin magance irin wadannan miyagun ayyuka.