’Yan sandan da aka yi garkuwa da su a Katsina sun kubuta

Hafsoshin ’Yan sanda 12 da aka yi garkuwa da su a titin Kankara zuwa Sheme a Jihar Katsina mako biyu da suka gabata sun kubuta kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana. An rawaito cewa an garzaya da ’yan sandan zuwa wani babban asibiti a birnin Gusau, Jihar Zamfara don duba lafiyarsu. Da zarar an […]

’Yan sandan da aka yi garkuwa da su a Katsina sun kubuta

Jami’an ‘Yan sanda

Hafsoshin ’Yan sanda 12 da aka yi garkuwa da su a titin Kankara zuwa Sheme a Jihar Katsina mako biyu da suka gabata sun kubuta kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.

An rawaito cewa an garzaya da ’yan sandan zuwa wani babban asibiti a birnin Gusau, Jihar Zamfara don duba lafiyarsu.

Wakilinmu ya tuntubi Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, Usman Nagogo, sai ya sada shi da Kakakin Rundunar na Kasa, Frank Mba.

“Ka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sanda na kasa saboda lamarin an mika shi zuwa shelkwatar ’yan sanda ta kasa”, Inji Nagogo.

Frank Mba, ya tabbatar cewa tara daga cikin jami’an sun kubuta daga hannun masu garkuwar.

An dai yi garkuwa da hafsohon ’yan sandar ne a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Zamfara don gudanar da wani aiki na musanman.

Wata majiya ta ce sai da masu garkuwar suka bukaci kudin fansa kafin su saki jami’an ’yan sandar.

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga