’Yan sandan duniya na neman Maina ruwa a jallo
Hukumar ’Yan sanda ta Duniya Interpol ta fitar da sanarwar neman tsohon Shugaban Kwamitin Cika-aiki kan Sake Fasalin Harkokin Fansho a Najeriya Alhaji Abdulrasheed Maina ruwa a jallo.Aminiya ta samu labarin an fitar da wannan sanarwa ce bisa bukatar haka daga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), wadda a ranar 18 […]
Hukumar ’Yan sanda ta Duniya Interpol ta fitar da sanarwar neman tsohon Shugaban Kwamitin Cika-aiki kan Sake Fasalin Harkokin Fansho a Najeriya Alhaji Abdulrasheed Maina ruwa a jallo.
Aminiya ta samu labarin an fitar da wannan sanarwa ce bisa bukatar haka daga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), wadda a ranar 18 ga watan Nuwamban bara ta rubuta wa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mista Solomon Arase tana bukatar taimakonsa don ya sanar da Hukumar ’Yan sandan Duniya cewa ana neman Maina wanda aka riga aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Tarayya kan wasu laifuffuka a ranar 10 ga watan Yulin bara.
Domin biya wa Hukumar EFCC bukata ne Mista Olushola Subair wanda Kwamishinan ’Yan sanda ne a Hukumar’Yan sandan Duniya a wata wasika da mai kwanan wata 11 ga Janairu, 2016 da ya aike ga Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Maguy a shaida wa hukumar cewa an dauki mataki kan bukatarta, kuma Hukumar INTERPOL ta fitar da sanarwa kamar yadda Aminiya ta samu labari.
A cikin wasikar Hukumar INTERPOL ta ce: “Ana sanar da ku cewa hukumar ta dauki matakan da suka wajaba a kan gudajjen wanda ake zargi kamar yadda kuka bukata daga Babbar Sakatariyar Hukumar INTERPOL da ke Lyon ta kasar Faransa. Kuma an buga sanarwar nemansa a takardar sanarwar nema ruwa a jallo ta Hukumar INTERPOL, kamar yadda ake bukata.”
Ana zargin Abdulrasheed Maina ne da hannu a yin almundahana da sace Naira biliyan biyu a lokacin da yake shugabancin Kwamitin Cika-aiki na Sake Fasalin Fansho.