’Yan sandan Ebonyi na tsare da basaraken gargajiya bisa zarginsa da satar tiransifoma
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ebonyi ta tabbatar da kama wani basaraken gargajiya na al’ummar Ipene,da ke Karamar Hukumar Biase Jihar Kuros Riba mai suna Cif Paulinus Ogbor, tare da wani tsohon dan sanda mai suna Onugh, bisa zargin su da satar na’urorin rarraba wuta wato tiransifoma. Kakakin rundunar DSP Lobeth Odah, ne ya sanar da […]
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ebonyi ta tabbatar da kama wani basaraken gargajiya na al’ummar Ipene,da ke Karamar Hukumar Biase Jihar Kuros Riba mai suna Cif Paulinus Ogbor, tare da wani tsohon dan sanda mai suna Onugh, bisa zargin su da satar na’urorin rarraba wuta wato tiransifoma.
Kakakin rundunar DSP Lobeth Odah, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abakalike. Ya ce, rundunar sojin Najeriya ta 13 da ke Kalaba, ta kama wadanda ake zargin a yankin Unwana Karamar hukumar Afikpo ta Arewa jihar Ebonyi shi yasa aka mika mana su domin ci gaba da binciken su.
Aminiya ta samu rahoton na’urar raba wutar ta al’umomin yankin Umuolo, Etana, Ubum, Edu da Ibini, sauran su ne: Afono da Urugbam da Ipene da Egbor dukkan su a karamar hukumar Biase, Jihar Kuros Riba. Jami’in ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, ”Lokacin da suka zo shingen duba ababen hawa da ke Unwana da jami’an suka tambaye su ina zasu kai na’urorin sai suka ce, musu na kamfanin raba wutar lantarki na Enugu ne can zasu kai su dan kwangilar da aka bashi kwangilar sayen su ne ya aike su .
Tambayoyin da jami’an sojin suka rika yi musu ba kakkautawa ce ya sanya aka gano cewa, satar na’urorin suka yi aka kama su akan hanyar.