’Yan sandan Gombe sun kuduri horar da matasa 400 a makarantun Jihar
Don ganin an ci gaba da samun raguwar aikata ta’addanci a tsakanin matasa, musamman ’yan bangar siyasa da ake kira Kalare a Jihar Gombe ya sa hukumar ’yan sanda a Jihar ta bullo da wani shiri na mayar da matasa har 400 da ba su iya kammala sakandare ba, ko aka kore su don su […]
Don ganin an ci gaba da samun raguwar aikata ta’addanci a tsakanin matasa, musamman ’yan bangar siyasa da ake kira Kalare a Jihar Gombe ya sa hukumar ’yan sanda a Jihar ta bullo da wani shiri na mayar da matasa har 400 da ba su iya kammala sakandare ba, ko aka kore su don su sami hanyar rayuwa tagari nan gaba.
Kwamishinan ’yan sandan jihar ne, Mista Austin I. Iwar ya bayyana hakan a lokacin da hukumar ta hada kan manyan jami’anta ta gudanar da wani taro na wuni daya don neman hanyar tallafa wa irin wadannan matasa.
Ya ce duk da ganin cewa Kalare dai su ne ’yan bangar siyasa kuma ba su da wani aiki sai ta’addanci amma a sakamakon hadin kai da hukumar ’yan sanda take samu daga wajen mutanen gari don shawo kan aika-aikar matasan hakan, ya sa an samu raguwar aika-aikarsu; inda ya ce a tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban bana, an samu rahoton aika-aika 87 ne kawai na ’yan ta’addar.
Ya kuma ce daga Yuli zuwa Agusta kawai da suka gabata, an samu aika-aikar ’yan Kalaren har guda 246, inda ya ce hakan ne ya bai wa hukumar tasu kwarin gwiwar ganin ta mayar da matasan makaranta tunda sun fara samun natsuwa.
Kwamishinan ya kara da cewa hukumarsa za ta hada kai ne da ma’aikatar ilimi ta jihar, don ganin irin wadannan matasa sun koma makaranta kasancewar da yawa daga cikinsu suna da fasahar da ta wuce su ci gaba da aikata bangar siyasa ko gararanba a kan tituna da tsakanin ’yan siyasa. Daga nan sai ya yi kira ga jama’ar gari da masu ruwa da tsaki wajen ganin sun ci gaba da taimaka wa ’yan sandan don tabbatar da ganin an sake samun raguwar ta’addancin a tsakanin matasan.