‘Yan sandan jahar Delta sun cafke barayin awaki

Rundunar  ‘yan sandan jahar Delta ta bayar da sanarwar cafke wata mota karama kirar Toyota camry makare da tumakin “sata”. Hukumar ‘yan sandan ta cafke mutananen lockacin da suke tafiya akan hanyar su Benin sun cika karamar motar da tumakai guda goma 11 wadanda ake zatan ba nasu ba ne. Kakakin rundunar ‘yan sanda ta […]

‘Yan sandan jahar Delta sun cafke barayin awaki
‘Yan sandan jahar Delta sun cafke barayin awaki

Rundunar  ‘yan sandan jahar Delta ta bayar da sanarwar cafke wata mota karama kirar Toyota camry makare da tumakin “sata”.
Hukumar ‘yan sandan ta cafke mutananen lockacin da suke tafiya akan hanyar su Benin sun cika karamar motar da tumakai guda goma 11 wadanda ake zatan ba nasu ba ne.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kalaba, Celestina Kalu ta gayawa manema labarai a garin Kalaba cewa ‘yan sandan sintiri suka cafke mutanen. “‘yan sanda dake sintiri a babbar hanyar sapele zuwa Benin ce suka cafke su bayan da motar mai lamba Edo 782 AP ta karaso wajen ‘yan sandan suke tsaye amma suka ki tsayawa. Wannan ya sa ‘yan sandan suka zarge su kuma suka bisu har dai suka cim masu.”
Rundunar ta ce da barayin suka ga an cimmasu sai suka ranta a na kare, suka bar motar da awakin a kan hanya.
Taci gaba da cewa “jami’an mu da suka zo wurin motar sun iske awaki 10 masu rai daya kuma matatta”. Rundunar ta sha alwashin zakulo barayin da suka gudu a duk ma inda suka boye.