’Yan sandan Jihar Kebbi sun gano inda miyagu ke boye makamai a daji
Rundanar ’yan sandan Jihar Kebbi ta gano wani wuri a cikin daji a kauyen Rafin-Kuka da ke karamar Hukumar Yawuri inda wasu miyagu suke ajiye bindigoginsu domin yin ta’ addanci. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Syebester Umeh ne ya bayyana haka ga manema labarai a hedikwatar ’yan sandan Jihar da ke Birnin Kebbi a lokacin da […]
Rundanar ’yan sandan Jihar Kebbi ta gano wani wuri a cikin daji a kauyen Rafin-Kuka da ke karamar Hukumar Yawuri inda wasu miyagu suke ajiye bindigoginsu domin yin ta’ addanci. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Syebester Umeh ne ya bayyana haka ga manema labarai a hedikwatar ’yan sandan Jihar da ke Birnin Kebbi a lokacin da yake gabatar da bindigogin ga manema labarai. Kwamishinan ya ce cikin miyagun makaman da suka samu akwai bindigogi kirar AK 47 uku da albarusai 178 da karamar bindiga da albarusanta 8 da sauran makamai, ya ce sun samu nasarar gano makaman ne sakamakon rahoton da wani mutum ne ya kai a ofishin ’yan sanda na Yawuri. Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar su rika hada kai da jami’an tsaro tare da kawo rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba. Ya ce jami’an tsaro ba za su samu cikakkiyar nasara ba, sai sun samu hadin kai da goyon bayan jama’ar gari.