Yan sandan Jihar Kuros Riba sun gargadi ’yan siyasa kan yawo da makamai

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta haramta wa duk wani dan siyasa a jihar da kw yawon kamfe yin amfani da  makami ko ’yan daba ko amfani da motocin da ba su da lamba. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Alhaji Hafiz Muhammad Inuwa ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da aka raba […]

Yan sandan Jihar Kuros Riba sun gargadi ’yan siyasa kan yawo da makamai

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta haramta wa duk wani dan siyasa a jihar da kw yawon kamfe yin amfani da  makami ko ’yan daba ko amfani da motocin da ba su da lamba.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Alhaji Hafiz Muhammad Inuwa ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ciki har da Aminiya a shekaranjiya Laraba. Ya ce, rundunarsa ba za ta lamunci duk wani dan siyasa da ya yi yawon kamfen a jihar nan ya yi amfani da miyagun makamai ko ’yan ta’adda domin tayar-da-zaune-tsaye ba.

Sanarwar ta Kwamishinan ’Yan sanda Muhammad Inuwa, ta ja kunnen duk wani dan siyasa da kada ya kuskura ya yi amfani da motar da aka sanya wa gilashinta wani abu da zai iya hana a gane wadanda ke ciki. “Duk wanda muka kama da aikata daya daga cikin laifuffukan da doka ta hana za mu kama shi mu kuma mika shi ga hukuma ta gaba,” inji shi.

Kwamishinan ya gargadi ’yan siyasa daga kowace jam’iyya a jihar su guji yin kamfe na vatanci ko yi wa juna yarfe da habaici ko kuma furta wata kalma da ka iya harzuka abokin takara.

Wakilinmu ya ce  a makonnin da suka gabata an sanya zare tsakanin magoya bayan Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar da APC mai adawa saboda zargin magoya bayan juna na  cire wa juna allunan kamfen din ’yan takararsu da fastocinsu a kan manyan hanyoyin shiga jihar da kuma wasu daga cikin unguwannin biranen jihar.

Sanarwar ta bukaci ’yan siyasa su  yi kamfe cikin lumana da kwanciyar hankali, su kauce wa aikata duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali ko barazana ga tsaro a jihar. “Ina shawartar ’yan takara su  yi kiyaye doka yayin yakin neman zave, kamar yadda dokar kasar ta tanada,” inji sanarwar.