’Yan sandan Jihar Nasarawa sun kama wadanda suka kashe Sarkin Mama
Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta kama mutum hudu da take zargi da hannu a kisan Mai martaba Sarkin Mama (Gwam Mama) Alhaji Zubariru Adamu da ke karamar Hukumar Wamba. Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a Lafiya, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Idris Ibrahim ya ce rundunar ta yi nasarar kama […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta kama mutum hudu da take zargi da hannu a kisan Mai martaba Sarkin Mama (Gwam Mama) Alhaji Zubariru Adamu da ke karamar Hukumar Wamba.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a Lafiya, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Idris Ibrahim ya ce rundunar ta yi nasarar kama wadanda ake zargin ne a Lafiya bayan bincike mai zurfi.
Wadanda ake zargin a cewar Kwamishinan sun hada da Bamai Mustapha da Jamilu Adoda da Auwal Adamu da kuma wanda ake wa lakabi da dan Borno. Ya ce makaman da aka gano daga wurinsu sun hada da bindiga kirar AK 47 da bindigogi kirar gida da bindigogin roba 11 da layu da sauransu.
A cewarsa tuni rundunar ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotu don hukunta su daidai da laifin da aka same su da shi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ’yan sandan suka tsare matar marigayi Gwam Mama da wata ’yarta bisa zargin hada baki da wasu mutane su zuba wa Sarkin guba a abinci ya ci ya mutu a lokacin da yake shirye-shiryen kara aure.