’Yan sandan Kaduna sun kama wadda ta sato yara uku daga Kano

Dubun wata barauniyar yara mai suna Lobe Ogar mai kimanin shekara 29 daga Jihar Ribas ya cika sakamakon kamata da ’yan sandan Jihar Kaduna suka yi kan zargin sato wasu yara uku daga Jihar Kano. Aminiya ta samu labarin cewa matar ta sato yaran ne a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano kuma tana cikin […]

’Yan sandan Kaduna sun kama wadda ta sato yara uku daga Kano
’Yan sandan Kaduna sun kama wadda ta sato yara uku daga Kano

Dubun wata barauniyar yara mai suna Lobe Ogar mai kimanin shekara 29 daga Jihar Ribas ya cika sakamakon kamata da ’yan sandan Jihar Kaduna suka yi kan zargin sato wasu yara uku daga Jihar Kano.

Aminiya ta samu labarin cewa matar ta sato yaran ne a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano kuma tana cikin mota a kan hanyarta ta zuwa Abuja kafin ta zarce garin Anacha ne dubunta ta cika.
Da yake gabatar da ita ga manema labarai a hedkwatarsu a Kaduna, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, SP Aminu Lawan ya ce wani daga cikin shugabannin tashar motar Kawo Kaduna ne ya sanar da ’yan sanda ta wayar tarho cewa suna zargin matar.
A cewar shugaban, direban motar da matar ta shigo daga Kano da yaran uku ne ya sanar da su bayan sun iso Kaduna cewa bai yarda cewa matar ce mahaifiyar yaran ba saboda wasu halaye da yaran ke nuna mata a cikin motar.
SP Lawan ya ce matar ta kasa ba da sahihiyar amsa kan tambayoyin da shugabannin tashar motar suka yi mata, wanda hakan ya sa suka kira ’yan sanda domin ci gaba da yi mata tambayoyi kuma daga bisani ta amsa cewa sato yaran ta yi daga Kano kuma Abuja za ta kai su.
Wacce ake zargi, Lobe ta ce wata kawarta mai suna Tina da ke zaune a Abuja ce ta tura ta ta sato mata almijirai za ta biya ta Naira dubu 350 a kan kowane yaro daya.
“Lokacin da na isa Hotoro ina zaune cikin Keke NAPEP sai na kira yaran su uku na ba su alawa daga nan sai na bukaci su shigo cikin Keke NAPEP din. Da suka shigo sai muka wuce tashar motar Sabon Gari inda na shiga motar zuwa Anacha da niyyar sauka a Abuja. Saboda kawata Tina wacce ta yi shekara bakwai da aure babu haihuwa ce ta bukaci in kawo mata yaran. Wannan ne karo na farko da na soma irin wannan sana’a. Kuma ba ta biya ni kudin ba, sai na kai mata yaran,” inji ta.
Mahaifin yaran wanda aka kira shi zuwa Kaduna mai suna Malam Muhammadu Sanusi cewa ya yi matarsa ce ta sanar da shi kwana uku da suka wuce cewa ba ta ga ’ya’yansa ba amma saboda ya san ba su cika yawo ba sai ya tsananta bincike a unguwarsu a Kano amma ba a gansu ba.
“Daga nan sai na sanar da ’yan sanda halin da ake ciki sai ga shi sun kira ni da misalin karfe 12:00 na ranar Alhamis cewa an kama wata mace da yara uku a Kaduna don haka in je in duba. Da na iso hedkwatar ’yan sandan Kaduna sai na tarar da ’ya’yana uku. Wato Nafi’u Sanusi mai shekara 6 da Khalid Sanusi mai shekara biyar sai Abdul Sanusi mai shekara hudu. Ina godiya ga Allah sannan ina godiya ga ’yan sanda da Allah Ya ba su nasarar kama wannan mata,” inji shi.
Ya shawarci masu mugun hali irin matar da su daina domin ko ba dade ko ba jima Allah zai tona musu asiri.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta cigaba da bincike domin gano abokan aikin matar don gurfanar da su gaban kotu.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi