’Yan sandan Kano sun lallasa ’yan Kannywood a wasan sada zumunta

’Yan sandan sun kuma lallasa ’yan TikTok da tubabbun ’yan daba.

’Yan sandan Kano sun lallasa ’yan Kannywood a wasan sada zumunta

Rundunar ’yan sandan Kano ta lallasa ’yan masana’antar fina-finai ta Kannywood a wasan sada zumunta da suka fafata ranar Alhamis.

Cikin wani sako da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce sun lallasa ’yan Kannywood din da ci 4-0 a wasan da kece-raini a filin wasa na Sani Abacha.

Kiyawa ya ce wasan ya samu halartar kwamishinan ’yan sandan jihar Muhammed Usaini Gumel da sauran manyan taurarin Kannywood.

Tawagar ’yan sandan bayan an tashi wasan

Hukumar ƴan sandan ta shirya wasan ne domin karfafa zumunci tsakaninsu da taurarin na Kannywood.

 

Tawagar ’yan wasan Kannywood

Kafin wannan wasa, ’yan sandan sun kuma fafata da kungiyar ’yan TikTok a Kano da kuma ta tubabbun ’yan daba, inda suka samu nasarar duka wasannin.

Kwamishinan ’yan sandan Kano yana gaisawa da ’yan kwallon gabanin soma wasa