’Yan sandan Kebbi sun kama ’yan ta’adda 11 a iyakar Zamfara
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 11 a Qaramar Hukumar Danko-Wasagu da ke kan iyakar jihar da Jihar Zamfara da ake zargi da aikata miyagun ayyuka. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim M. Kabiru ne, ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhumar ga ’yan jarida a hedikwatar ’yan […]

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 11 a Qaramar Hukumar Danko-Wasagu da ke kan iyakar jihar da Jihar Zamfara da ake zargi da aikata miyagun ayyuka.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi Alhaji Ibrahim M. Kabiru ne, ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhumar ga ’yan jarida a hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Birnin Kebbi.
Kwamishinan ya ce mutum 11 da aka kama ana tuhumarsu ne da kai hari a wani gari da ake kira Kaboro inda suka kashe mutum biyar a cikin garin, kuma mutum 10 daga cikin su ’yan asalin Jihar Zamfara ne daya kuma dan asalin Jihar Kebbi ne mazaunin Jihar Zamfara.
Alhaji Ibrahim Kabiru ya ce cikin wadanda aka kama akwai Lawal Ibrahim da Nasiru Lawali da Yahaya Mohammed da Haliru Shantali da Hussaini Hamisu da Mohammed Nuhu.
Sauran su ne Habibu Sani da Rilwanu Mohammed da Mohammed Sanusi da Mohammed Bara’u da kuma Abubakar Haruna, inda ya ce sun kama su da bindigogi biyar da ake kira wagila qirar gida.
Ana sa wa wannan bindiga fulogin babur ne a matsayin harsashi an kuma kama su da cebura 4 da gatura 4 da kuma wasu makamai.
Ya ce da zarar sun gama bincike za su tura wadanda ake zargi zuwa kotu domin yi musu hukuncin da ya dace.
Kwamishinan ya ce umarnin da Sefeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya bayar cewa duk wanda ke riqe da bindiga ba bisa qa’ida ba ya hanzarta kai ta ofishin ’yan sanda mafi kusa, ya sa sun karbo bindigogi qirar AK 47 guda 15 da kuma wagila manya da qanana guda 14 da qaramar fistol daya da maqunsan harsasai 32 da albarushi 650 masu girman milimita 7.62d 39.
Kwamishinan ya ce zai dauki matakin da ya kamata domin qara wa jami’ansa qwarin gwiwa don samar wa mutanen Jihar Kebbi damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali musamman a yankunan da suke kan iyaka da Jihar Zamfara.