’Yan sandan Kuros Riba sun gabatar da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane

Rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba ta gabatar wa manema labarai wasu kasurguman masu laifi guda 15  da ake zargi da aikata  sace mutane ana garkuwa da su, domin kudin fansa da kuma fashi da makami da suka addabi garin Kalaba,  babban birnin jihar da kewayensa, musamman yadda suka mayar da  garin Kalaba mazaunansa na […]

’Yan sandan Kuros Riba sun gabatar da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane
’Yan sandan Kuros Riba sun gabatar da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane

Rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba ta gabatar wa manema labarai wasu kasurguman masu laifi guda 15  da ake zargi da aikata  sace mutane ana garkuwa da su, domin kudin fansa da kuma fashi da makami da suka addabi garin Kalaba,  babban birnin jihar da kewayensa, musamman yadda suka mayar da  garin Kalaba mazaunansa na cikin zullumi.
Da ya gabatar da su a harabar ofishin ’yan sandan kwamishinan ’yan sandan Jihar Kuros Riba, Jimoh Ozi-Obeh, ya ce yadda aka yi wadanda  ake zargi suka shiga komar su ta hanyar kiran gaugaw a na neman kawo dauki da ake yi masu ne ya sa har suka yi katarin kama su daya-bayan daya, a sassa daban-daban na jihar, inda biyu daga cikinsu an same su da aikta laifin kama mutane suna yin garkuwa da su, sannan kuma saura daga masu fashi da makami da masu fisge da kuma yi wa mutane kwantan bauna suna masu nsata.
Daga nan ya  kara jadda da aniyar rundunarsa na ci gaba da yaki da duk wasu masu aikata miyagun hali da suka addabi jihar. Ya bukaci duk fa wata nasara da suke samu sai  da hadin kan jama’a, tare da tona asirin duk wani mugu da ba su  saki jiki da shi ba.
A wata sabuwa ranar Litinin din da ghabata wata mota kirar Toyota ta kurda karkashin wata babbar mota kwantena, da aka ajiye gefen hanya a layin Bagobiri da ke unguwar Hausawa Kalaba. Ganau ya shaida wa Aminiya cewa, hadarin ya yi sanadiyar mutuwar yaron motar mai suna Mustapha Unguwar dinya,karaye Jihar Kano.  Shi kuwa direban karamar motar da ya kara ya samu mummunan rauni a jikinsa.
“Direban karamar motar ya kwaso motar a guje, kuma cikin maye yake koda aka je ceton su aka gane haka, sai ya bi takan yaron motar da yake kokarin rufe bayan babbar motar tasu. Bayan da ya sa alamar ja da direba idan ya ajiye mota za ta nuna masa akwai wata a jiye gabansa, don ya ankara, nan take ya hada da yaron motar ya bi ta kansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwar sa. Shi kuma ya kai kansa wurin ’yan sanda,” a cewar majiyaru.