Yan sandan Legas sun yi tayin Naira miliyan biyar ga wanda ya tona asirin ’yan fashi
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Kayode Aderanti ya nuna bacin ransa dangane da yadda ’yan fashi da makami suka kai wa bankuna biyu hari har suka kwashe miliyoyin Naira a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas a ranar Laraba ba tare da ’yan sanda sun kama su ba. Saboda haka ya ce rundunar za ta […]
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Kayode Aderanti ya nuna bacin ransa dangane da yadda ’yan fashi da makami suka kai wa bankuna biyu hari har suka kwashe miliyoyin Naira a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas a ranar Laraba ba tare da ’yan sanda sun kama su ba.
Saboda haka ya ce rundunar za ta binciki jami’an ’yan sandan da ke aiki a yankin Ikorodu a lokacin da ’yan fashin suka kai harin.
Ya yi furucin ne yayin da ya kai ziyara yankin bayan aukuwar lamarin, inda ya bayyana lamarin da abin bakin ciki.
“Na zo ne tare da jami’an tsaro na jihar nan kuma mun zo ne don mu ga yadda za mu bullo wa lamarin tare. Saboda haka, muna da tabbacin samun nasarar gano bakin zaren. Don haka za mu binciki yadda lamarin ya auku musamman halin da jami’anmu suka nuna yayin da ’yan fashin suka kawo harin. A halin yanzu muna binciken ayyukan da ke gudana a tashar ruwan yankin da kuma hanyoyin da ’yan fashin suka yi amfani da su wajen guduwa. Ina mai tabbatar muku da cewa babu a asarar rayuka.” Inji shi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Kenneth Nwosu, ya ce rundunar ta yi alkawarin bayar da ladar Naira miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da muhimmin bayanin da zai kai ga kamo ’yan fashin.
“Hedikwatar rundunar ’yan sandan Jihar Legas za ta ba duk mutumin da ya ta bayanin da zai taimaka a kamo ’yan fashin har Naira miliyan biyar.”
’Yan fashin sun yi wa bankin Zaneth da bankin First Bank da ke unguwar Ebute-Ipakodo da ke yankin Ikorodu dirar mikiya a lokaci guda, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi tare da kwashe kudin bankunan.
’Yan fashin wadanda sun kai kimanin su 16, dukkansu matasa ne kuma suna bin ummarnin wata matashiya ne sannan kuma sun ci karensu ba babbaka ba tare da jami’an tsaron sun kalubalence su ba.
Shaidu da suka gane wa idonsu yadda lamarin ya auku sun bayyana cewa ’yan fashin sun yi wa mutane da dama rauni sakamakon harbin da suka rika yi sannan sun kwashi kudi da yawa daga bankunan.
Daga bisani suka sanya wa motocin da suka zo wurin da su wuta, inda suka yi amfani da tashar jiragen ruwa da ke kusa da wurin suka sulale da kudin da suka sata.
Wani mazaunin yankin Ikorudu, Malam Abdullahi ya bayyana wa Aminiya cewa kura ta lafa kuma mutanen yankin sun ci gaba da gudanar da al’amaransu kamar yadda suka saba. Ya ce, sai dai bankunan sun kasance a rufe tare da jibge jami’an tsaro a harabarsu.
Har lokacin hada wannan rahoto bankin Zaneth da bankin First bank ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da asarar da suka yi. Wannan ba shi ne karo na farko ba da ’yan fashi ke kai hari ga bankunan da ke yankin Ikorodu.
A kwanakin baya ma ’yan fashin sun yi wa bankunan yankin dirar mikiya amma sai dai ba su samu nasara ba sosai.