’Yan sandan Ribas sun gano gidan kyankyasar yara

‘Yan sanda a Jihar Ribas sun ce sun gano wani gida da ake ajiye ’yan mata ana lalata da su idan sun yi ciki sun haihu sai a sayar da jariran. An gano gidan ne a Unguwar Woji da ke garin Fatakwal makon jiya. A yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu musamman ana […]

’Yan sandan Ribas sun gano gidan kyankyasar yara

Jariran da wadanda ake zargi da mallakar gidan kyankyasar

‘Yan sanda a Jihar Ribas sun ce sun gano wani gida da ake ajiye ’yan mata ana lalata da su idan sun yi ciki sun haihu sai a sayar da jariran. An gano gidan ne a Unguwar Woji da ke garin Fatakwal makon jiya.

A yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu musamman ana yawan samun gidajen kyankyasar yara da ake fakewa cewa asibiti ne ko gidan marayu ana sayar da jarirai.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas Nnamdi Omoni ya ce, “Bayanan sirri da aka sanar da rundunar ne ya kai ta ga samun wannan nasara.”

Ya ce sun kubutar da jarirai 24 masu shekara daya zuwa biyu da haihuwa.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ribas, Mustafa Dandaura ya ce rundunar na ci gaba da neman masu hannu a kafa gidan sayar da jariran domin kai su kotu su fuskanci hukunci.