’Yan sandan Ribas sun kama masu laifi mutum 28

Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta damke wasu manyan masu laifi mutum 28 da ake zaton su ne ke hana jihar sakat. Daga cikin masu laifin da ake zargi sun hada da mutum 13 wadanda ake zargin su da kwarewa wajen kama mutane suna yin garkuwa da su, da ma kitsa yadda za a kama […]

’Yan sandan Ribas sun kama masu laifi mutum 28
’Yan sandan Ribas sun kama masu laifi mutum 28

Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta damke wasu manyan masu laifi mutum 28 da ake zaton su ne ke hana jihar sakat. Daga cikin masu laifin da ake zargi sun hada da mutum 13 wadanda ake zargin su da kwarewa wajen kama mutane suna yin garkuwa da su, da ma kitsa yadda za a kama a karbi kudin fansa. Su kuwa ragowar mutum 15 ana zargin su da aikata fashi da makami a sassa daban-daban na jihar har ma da wajenta , an kuma kama su ne da wasu harsasai 60 .

Ahmad Muhammad Kaliya, kakakin rundunar ne ya sanar wa manema labarai wawan kamun da suka yi.
Da yake yi wa Aminiya karin haske game da nasarorin da suka samu, Ahmad Kaliya ya ce “mutum 13 masu aikata garkuwa da mutane ne, domin karbar kudin fansa, yayin da ake zargin mutum 15 da aikata laifin fashi da makami. An kama albarusai 44 a hannunsu da bindigogi bakwai da kuma karin wasu motocin da suka sata guda bakwai.”
Ya ce har wayau wata sabuwar dabara da masu kama mutanen ke yi wajen wawashe asusun kudin ajiyar wanda suka kama suke garkuwa da shi, inda suke amfani da katin debi da kanka, wato ATM su zare duk kan abin da wanda suka kama ya mallaka a asussunsa.
“wani daga cikin wadan da suka kama suka yi garkuwa da su ne ya bayyana mana haka,” inji shi .
Har yanzu dai shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar ribas Okay Wali babu duriyarsa, amma jami’in ’yan sandan yace rundunar batayi kasa a gwiwa ba tana bakin kokari har sai ta gano maboyar da aka boyeshi ta kuma cafko masu laifin.