’Yan sandan Sakkwato sun kama barayi da ’yan fashi 11
’Yan sandan Jihar Sakkwato sun samu nasarar kama barayin mota da ’yan fashi da makami 11, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Salisu Fagge Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce a ranar 4 ga Mayu wasu masu suna Uche Okpara da Ndubuisi Okafor da ke zaune a unguwar Difiloma […]
’Yan sandan Jihar Sakkwato sun samu nasarar kama barayin mota da ’yan fashi da makami 11, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Salisu Fagge Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce a ranar 4 ga Mayu wasu masu suna Uche Okpara da Ndubuisi Okafor da ke zaune a unguwar Difiloma Sakkwato ake zargin sun sace wata mota kirar Toyota Camry suka tafi da ita garin Asaba ta Jihar Delta kafin su jami’ansu su kama su ta hanyar samun bayanan sirri.
Kwamsihina Salisu Fagge ya ce bayan sun kama su ne suka samu labarin mai yi musu makullin mota na musamman a duk lokacin da za su je satar mota mai suna Nasiru Mijiyawa wanda ma’aikaci ne a rundunar tsaro ta jihar da aka fi sani da ‘Sokoto Marshal.’
Kwamishina Fagge ya ce a ranar Jumu’ar da ta gabata sun kama wani mai suna Jamilu Ahmad da ake zargi da kasancewa cikin wadanda suka yi fashi da makami a Unguwar Rijiya da ke Sakkwato, inda suka jikkata mutum biyu tare da salwatar da wayar hannun wani mutum kuma bayan kama shi ya nuna sauran mutum hudu da suke tare da aka same su da waya da kuma gariyo.
Kwamishinan ya ce a ranar 4 ga Yunin nan sun samu nasarar kama Yenta Garba daya daga cikin shugabannin wadanda ake zargi da fashi a kauyen Gidan Daji a yankin Achida da ke karamar Hukumar Wurno, inda aka kashe daya daga cikinsu. Kuma ya taimaka musu da bayani sun kama mutum biyu daga cikinsu Bami Shehu da Shehu Abdullahi da ake wa lakabi da dan Ilela, ya ce da zarar sun kammala bincike za su kai su kotu don yi musu hukunci.