’Yan sandan shiyya ta shida sun samu nasarar kakkabe batagari
Shiyya ta shida ta rundunar ’yan sandan Najeriya ta bayyana nasarar kakkabe ayyukan bata gari da kuma dakile wasu, cikin kankanin lokaci, a wata biyu kacal, har da kubutar da wasu ’yan kasar Sin mutum biyu da aka yi garkuwa da su, da ma karin wasu nasarori masu tarin yawa, jim kadan da kama aiki […]
Shiyya ta shida ta rundunar ’yan sandan Najeriya ta bayyana nasarar kakkabe ayyukan bata gari da kuma dakile wasu, cikin kankanin lokaci, a wata biyu kacal, har da kubutar da wasu ’yan kasar Sin mutum biyu da aka yi garkuwa da su, da ma karin wasu nasarori masu tarin yawa, jim kadan da kama aiki a matsayin Mataimakin Sufeto Janar ‘yan sandan Najeriya, mai kula da shiyya ta shida, wadda ke da hedkwata a Kalaba ta Jihar Kuros Riba.
A cewar Mark A. Idakwo, daga ciki an kama sama da mutum 52, wadanda aka cafke bisa zargin su da aikata miyagun laifuka. Mataimakin Sufeto Janar din ya bayyana wa manema labarai hakan a kalaba.
Shiyya ta shida ta kunshi Jihohin Akwa Ibom, kuros riba, Ebonyi, da kuma ribas a wadan nan jahohi kamar yadda mataimakin ya fada “masu laifin sun hada da fashi da makami, kama mutane a yi garkuwa da su, don neman kudin fansa; ga kungiyar asiri, da kuma fataucin mutane aka kama lokuta daban-daban a jahohin shiyyar.
Da yake bayar da bayanin dalla-dalla a Jihar Akwa Ibom kadai an kama mutum 23 da ake zargin su da aikata laifin fashi da makami da safarar yara da ayyukan kungiyar asiri da sata da makamantan su, “Munyi katarin kubutar da yara hudu daga hannun masu safarar yara kanana yaran, wadanda suka hada da Goodness Godwin Sunday, da kuma ceto ran wani jariri dan kwana daya da haihuwa da uwarsa ta binne da rai, an kama uwar, kuma an ceto jaririn da ransa. Sai kuma Dabid Kufre Eyo Sunday dan shekara biyu da rabi da haihuwa wadanda duk safarar su,” inji shi.
Rundunar tayi katarin ganowa tare da kwace kudi zunzurutun naira 33,000 da kuma Naira milyan takwas da dubu 900, a hannun wasu ’yan fashi. Sauran su ne mota kirar Nissan, mai lamba PST 813 BS da mota kirar Toyota, mai lamba 813 BS da kuma mota kirar Audi ita ma mai lamba AKP 24 AA. Har wa yau, an kwato mota mai lamba MDS 541 dC.
A Jihohin Akwa ibom da Kuros Riba kuwa, mataimakin sufeton ’yan sanda mai kula da shiyya ta shida, ya ce: “Mutum bakwai, inda hudu daga cikinsu ake zargin su da laifin fashi, mutum daya kisan kai ake tuhumarsa da aikatawa, yayinda mutum biyu kuma laifin sata.
Sannan an kubutar da wata budurwa, tare da kwato wata mota kirar Toyota corolla sai laifin kisan kai mutum daya.
A jahar Ebonyi kuma mutum 32 aka kama bisa zargin hada tawagar ’yan fashi suke gudanar da danyar sana’ar su
Aminiya ta tambaye shi lura da aka sarin kubutar da wadanda ake garkuwa da su sai an biya kudin fansa ko Naira nawa aka bayar kafin a kubutar da mutanen? Mataimakin sufeton ’yan sandan, ya ce “Ko kwandala ba a kashe ba; babu wani abu da aka bayar bil hasalima daya daga cikin su ne ma ya shigo gari, ya saya musu abinci, inda aka kamashi; shi ne ya sanar wa ragowar ga inda yake so su zo, su karbi kudin fansa; suna zuwa aka yi musu kofar rago aka kama su.”