’Yan sandan sun gano nakiya tun zamanin yakin basasa

Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ta gano wata nakiya da aka binne a kasa tun zamanin da aka yi yakin basasar kasar nan  a wata unguwa mai suna Unity da ke  birnin Enugu shekara sama da  talatin  yanzu da gama yakin. Yadda aka yi ma har ido ya kai wurin shi ne wasu leburori da […]

’Yan sandan sun gano nakiya tun zamanin yakin basasa

Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ta gano wata nakiya da aka binne a kasa tun zamanin da aka yi yakin basasar kasar nan  a wata unguwa mai suna Unity da ke  birnin Enugu shekara sama da  talatin  yanzu da gama yakin.
Yadda aka yi ma har ido ya kai wurin shi ne wasu leburori da ke aikin gini a wannan unguwa ce suka ga abin yayin da suka hako shi. Ganinsa ke da wuya, sai aka sanar wa jami’an tsaro da ke aikin ko-ta-kwana a yaki da masu kama mutane suna garkuwa da su domin karbar kudin fansa. ’Yan sandan suka garzaya wurin suka kwakulo makamin suka tafi da shi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar ta Enugu Ebere Amaraizu ya shaida wa manema labarai a ofishinsu cewa, “ Hakika an gano wannan abu ne mai kama da bam kuma ba tare da ya fashe ba aka yi katarin cire shi daga wajen. Dangane da haka muke gargadin al’ummar da ke wannan kewayen da cewa da zarar sun ga wani abu daban da ba su gane masa ba, kada su yi karambanin sai sun san ko mene ne domin kar su afka wa nakiya da ba ta riga ta fashe ba.”
Wannan shi ne karo na biyu da aka gano tsohon makami a wannan yanki, na farko an same shi ne a yankin Umuhu.