‘Yan sandan sun kama wadda ta sayar da danta a Filato
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wata mata da ta sayar da danta da wadansu mata biyar da ake zargi da laifin fataucin kananan yara. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Isaac Akinmoyede ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar wa ’yan jarida wadanda ake zargin a hedkwatar rundunar da ke garin Jos. Kwamishinan […]
Matan da ake zargi da fataucin qananan yara tare da waxansu da ake zargi da aikata laifuffuka a Jihar Filato.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta kama wata mata da ta sayar da danta da wadansu mata biyar da ake zargi da laifin fataucin kananan yara.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Isaac Akinmoyede ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar wa ’yan jarida wadanda ake zargin a hedkwatar rundunar da ke garin Jos.
Kwamishinan ya bayyana sunayen mata da ake zargi da Rose Adams mai shekara 25 da Mildred Bakwo mai shekara 34 da Lisa Yisa Yelkopba mai shekara 35 da Fatima Abdul mai shekara 20 da kuma Christiana Ochuba mai shekara 32.
Kwamishinan ya ce a ranar 23 ga Augustan da ya gabata ne, wani mutum mai suna Chidi Daniel da ke zaune ne a Unguwar Jenta Mangoro a garin Jos ya kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na A Dibision cewa a ranar 31 ga Yulin bara, matarsa mai suna Rose Adams ta bar gidansa da ke garin Dadin Kowa, a Karamar Hukumar Jos ta Kudu tare da yaranta biyu Chinedu Daniel dan shekara daya da wata 8 da Chubuike Daniel dan shekara daya.
“Mai korafin ya yi bayanin cewa matar tasa ta dawo gida a ranar 23 ga watan Agusta da Chinedu Daniel kadai, ba tare da daya dan uwansa Chibuike Daniel ba. Lokacin da ya tambaye ta, ina ta bar Chibuike Daniel sai ta ce masa ta bayar da shi ga wata mata, da take aiki a wata gidauniyar kula da kananan yara,” inji shi.
Kwamishinan ya ce da ’yan sanda suka ci gaba da bincike, sai suka gano cewa matar ta sayar da danta ne ga wata mata mai suna Christiana Ochuba da ke zaune a hanyar Rukubu da ke garin Jos.
Kwamishinan ya ce da suka ci gaba da bincike ne, sai suka kai ga kama sauran matan da ake zargi da fataucin yara.
Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.