’Yan sandan Taraba na farautar tsofaffin kwamishinoni

’Yan sanda sun fara farautar tsofaffin kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar bayan da gwamnatin jihar a karkashin Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi ta bayar da umarnin kama duk wani tsohon kwamishinan da ya ki mayar da motar gwamnati da ya yi amfani da ita […]

’Yan sandan Taraba na farautar tsofaffin kwamishinoni
’Yan sandan Taraba na farautar tsofaffin kwamishinoni

’Yan sanda sun fara farautar tsofaffin kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar bayan da gwamnatin jihar a karkashin Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi ta bayar da umarnin kama duk wani tsohon kwamishinan da ya ki mayar da motar gwamnati da ya yi amfani da ita a lokacin yake mulki.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa zuwa ’yan sandan sun kama wani tsohon kwamishina daya yayin da wasu suka shiga wasan buya.
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa tun farkon hawan Alhaji Sani danladi ya umarci tsofaffin kwamishinonin su mara wa dan takararsa Mista Darius Ishaku baya, amma da yawa daga cikinsu suka ki amincewa da hakan.
Majiyar ta kara da cewa wannan ya sa Mukaddshin Gwamnan ya fusata inda ya kafa wani kwamiti don karbo motocin daga hannun kwamishinonin.
Gwamnatin jihar ta ba kwamitin ikon ya bi gidajen tsofaffin kwamishinonin ya karbo motocin ko ta halin kaka kuma kwamitin yana da ikon kama duk wani tsohon kwamishina ko iyalinsa in har suka ki ba ’yan kwamitin hadin kai.
Wakilinmu ya gano cewa a makon jiya ’yan kwamiti sun kama ’yar tsohon Kwamishinan Watsa Labarai Mista Atai a lokacin da suka je gidansa ba su iske shi ba.
Shugaban kwamitin Malam Abdulrazak ya shida wa wakilinmu cewa kwamitinsa na da ikon kama duk tsohon kwamishinan da ya ki mayar wa gwamnati motar da aka ba shi a lokacin da yake ofis.
Tsofaffin kwamishinonin suna kukan cewa ana yi musu bita da kulli ne kawai domin sun ki su mara wa dan takaran da gwamnati ke so Mista Darius Ishaku baya.
daya daga cikin tsofaffin kwamishinonin da bai so a fadi sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa akwai yarjejiniya a tsakaninsu da gwamnati cewa za a cire kudin motar daga albashinsu su mallaki motocin bayan sun bar ofis.
Ya ce ba shakka ’yan sanda sun kama ’yar tsohon kwamishinan watsa labarai domin ta yi wa ’yan kwamitin barazana a lokacin da suka nemi a gudanar da bincike a gidansu don a gano ko tsohon kwamishinan yana boye a ciki.
Abdurazak ya kara da cewa dole tsofaffin kwamishinonin su maida wa gwamnati motocin domin da kudin jama’a aka saya. Ya ce an kama tsohon kwamishina daya kuma an karbo motoci takwas.