’Yan sandan Yobe sun kama wadanda ake zargi da fyade da luwadi
Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ta gabatar da wadansu mutum 12 da ake zargi da aikata fyade da luwadi da fashi da makami a sassan jihar.Da ya ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar ’yan sandan da keDamaturu, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Zannah Muhammad Ibrahim ya ce rundunarsa ta shirya […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ta gabatar da wadansu mutum 12 da ake zargi da aikata fyade da luwadi da fashi da makami a sassan jihar.
Da ya ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar ’yan sandan da ke
Damaturu, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Zannah Muhammad Ibrahim ya ce rundunarsa ta shirya tsaf don kama mutanen da ke kokarin kawo barna a cikin al’umma.
Wadanda ake zargin sun hada da mutum uku da ake zargi da aikata luwadi sai mutum biyar da ake zargi da yunkurin yin fyade ga yaka kanana, cikinsu har da wani tsoho mai shekara 62, sai kuma mutum hudu da ake zargi da aikata laifin fashi da makami da kuma wani mutum da aka kama da makami.
Kwamishinan ya ce, dukan wadanda ake zargin nan ba da jimawa ba za a kai su gaban kotu don fuskantar hukunci.
Kwamishina Zannah ya gargadi jama’a su guji aikata laifuffukan da suke kokarin zama gama-gari musamman luwadi da fyade.