’Yan Sara-Suka suka sare hannun dayansu
Rikici a tsakanin matasa ’Yan Sara-Suka ya jawo sare hannun daya daga cikinsu mai suna Ali Magaji mai shekara 18. Yaran dukkansu makwabtan juna ne, Ali wanda aka sare wa hannun yana zaune ne a Layin Alba Bello Tudun Jukun, shi kuma wanda ake zargi da sare masa hannun mai suna Muhammad Umar dandandan yana […]
Rikici a tsakanin matasa ’Yan Sara-Suka ya jawo sare hannun daya daga cikinsu mai suna Ali Magaji mai shekara 18. Yaran dukkansu makwabtan juna ne, Ali wanda aka sare wa hannun yana zaune ne a Layin Alba Bello Tudun Jukun, shi kuma wanda ake zargi da sare masa hannun mai suna Muhammad Umar dandandan yana zaune ne a Layin Mahauta, Tudun Jukun da ke Gundumar Tukur-Tukur a karamar Hukumar Zariya.
Wani mai suna Iliya Shehu ya shaida wa Aminiya a unguwar cewa yana isa Layin Mahauta da misalin karfe goma saura na dare ranar da aka ga watan azumin Ramadan, sai ya ga samari suna ta gudu cewa an sare wa wani hannu. “To sai muka tsaya muka duba yadda lamarin yake sai muka ga ashe duk yaran na gida ne ke fada a tskaninsu. An ce wanda aka sare wa hannu su ne suka yiwo zuga domin zuwa tare wa wani abokinsu fada kowanne da gariyo da adda a hannunsa, wanda aka zo domin fada da shi ya samu sa’ar sare wa daya daga cikinsu hannu,” inji shi.
Wakilinmu ya ziyarci Ali Magaji da ke kwance a asibitin Wusasa, don jin abin da ya sa aka guntule masa hannu, inda ya ce a ranar da aka ga wantan azumin bana sun fito suna murnar ganin wata sai wani yaro mai suna Muhammad Umar dandandan ya tare su ya ce sun zo tonon fada ne, saboda akwai tsama a tsakaninsa da abokinsu mai suna Mustafa. “Don haka sai ya hau mu da sara ban ankara ba sai na ji hannuna a kasa. Ba gaskiya ba ne da mutane ke cewa mun yi masa takakkiya ce domin mu yi fada da shi. Mun fito murnar ganin watan azumi ne wannan shi ne gaskiyar magana. Domin ni dalibi ne a aji uku a makarantar sakandare kuma tunda mahaifina ya rasu ina sa’ar fanalbita ne don haka ni ba dan sara-suka ba ne,” inji shi.
Yayar Ali mai suna Hajara Magaji da take jinyarsa, ta bayyana wa wakilinmu cikin kuka cewa, “A gaskiya an kware mu, domin mu marayu ne iyayenmu duk sun rasu don haka ka ga ni nake jinyarsa kuma kanena ba dan sara-suka ba ne, tunda nake bai taba jawo min matsala ba, ga shi yanzu an nakasa shi. Don haka ina kira a bi masa hakkinsa,” inji ta.
Dokta Uwadia Gilbert Udomi babban likitan da ke kula da Asibitin Wusasa ya ce yadda aka kawo hannun yaron ya kai wani matsayi da ba ya da kyan gani kuma jini ya zuba sosai amma sun shawo kan matsalolin hannun yanzu yana karbar magani kuma zai samu sauki nan ba da dadewa ba.
Wani dan sanda da bai so a ambaci sunansa, ya ce sun samu labarin amma kafin su je wadanda suke rikicin sun gudu, sai wanda aka sare wa hannun kawai ne bai gudu ba, shi ma saboda sare hannunsa ne da aka yi, amma duk sun san wadanda suka yi aika-aikar, kuma sun baza komarsu za su kamo su.