’Yan Sara-Suka sun addabi mutanen garin Bauchi
Mazauna cikin garin Bauchi na fama da fargaba sakamakon yadda matasa ’yan-sara-suka suke fitowa suna far wa jama’ar da ba su san hawa ba ba su san sauka ba, ta yadda suka rika raunata mutane suna kwace musu dukiyoyinsu, yayin da wadansu kuma suka rasa rayukansu. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai […]
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, ALi A. Janga
Mazauna cikin garin Bauchi na fama da fargaba sakamakon yadda matasa ’yan-sara-suka suke fitowa suna far wa jama’ar da ba su san hawa ba ba su san sauka ba, ta yadda suka rika raunata mutane suna kwace musu dukiyoyinsu, yayin da wadansu kuma suka rasa rayukansu.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga gane adadin yawan wadanda suka rasa rayukansu ba, duk da cewa Rundunar ’yan sanda a jihar ta ce mutane biyu ne suka rasa rayukansu a farmakin ’yan-sara-sukan daban-daban, wadanda suka ji ciwo kuwa ba a kammala tantance su ba amma mazauna Unguwar Nassarawa Bakaro da Doya da Kofar Gombe da Unguwar Abujan Kwata sun ce wadanda suka rasu sun kai mutum biyar.
Farmakin ya fara ne tun bayan da aka kammala zaben Shugaban Kasa da na ’Yan Majalisun Tarayya aka fara samun matsalar dawowa da aikace aikacen ta’addanci na ’yan-sara-suka a cikin garin Bauchi kodayake kafin lokacin ma suna yin fadace-fadace da junansu daga lokaci zuwa lokaci.
Rikicin dai ya fara fitowa fili ne a ranar Laraba 19 ga Fabrairun day a gabata, inda wasu matasa suka fito suna murnar cin zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sai wadannan ’yan-sara-suka suka fito da wukakensu suka cire kunnen Muhammadu Harisu, wani matashi dan shekara 19 da ke Unguwar Nassarawa Bauchi. Akwai rahotannin da ke cewa sun kashe mutane biyu kuma sun ji wa mutane da yawa rauni, har ma sun fasa motar wani mutum.
Harisu ya shaida wa manema labarai cewa su dai wadannan ’yan-sara-suka sun zo ne kawai suka far wa mutane da sara da duka, shi ma yana zaune sai wadansu su hudu daga cikinsu suka far masa don kafin ma su zo wurinsa sun far ma wasu.
Ya ce lokacin da suka zo sai suka sare shi a bayan hannu suka kuma yanke masa kunne. Ya yi kokarin gudu amma sun riga sun sassare shi a hannu da baya da kuma kunnen yana ta zubar da jinni, shi ne ya shiga cikin wani kantin sayar da magani, inda a wajen ne aka rufe masa raunin don ya tsaida jinin da ke kwararara daga kunnensa. Daga bisani kuma aka kai shi asibitin tashar babiye, inda aka sake yi masa jinyar kunnen. Ya ce yana ji da kunnen amma ba sosai ba kuma yana jin radadin zafi sosai.
Wani lauya wanda ya tsaya takara a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, a karkashin inuwar Jam’iyyar PRP a zaben da ya gabata, Abubakar Sadik Idris ya ce shi ma matasan sun shiga gidansa a Unguwar Nassarawa suka far wa mutane, ciki har da kanwarsa mai dauke da juna biyu.
Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar ya ce sun sami labarin wannan farmakin mutane da ’yan-sara-suka suke yi da wukake da sanda, ya ce daga samun rahoton sai suka tura jami’ansu, wadanda suka shawo kan lamarin, sai dai an yi wa mutane uku rauni kuma ’yan sanda sun kai su asibiti, inda aka yi musu jinya aka sallame su.