’Yan Sara-Suka sun addabi Zamfara
Mazauna Gusau babban birnin Jihar Zamfara sun koka kan yawan kashe-kashe da matasa ’yan Sara-Suka da suka dauki hakan sana’a ke yi a halin yanzu. Lamarin ya sa al’ummar Unguwar Tudun Wada sun kai kokensu ga Majalisar Jihar.Baya ga Unguwar Tudun Wada akwai unguwanni kamar Tullukawa da Kan-Wuri da Bakin Gulbi da Nasarawa da Hayin […]
Mazauna Gusau babban birnin Jihar Zamfara sun koka kan yawan kashe-kashe da matasa ’yan Sara-Suka da suka dauki hakan sana’a ke yi a halin yanzu. Lamarin ya sa
al’ummar Unguwar Tudun Wada sun kai kokensu ga Majalisar Jihar.
Baya ga Unguwar Tudun Wada akwai unguwanni kamar Tullukawa da Kan-Wuri da Bakin Gulbi da Nasarawa da Hayin Malam Sani da Filin Idi da kuma Baifas da sauransu da suke fama da wannan matsala.
A kwanakin ’yan Sara-Sukan sun kama wani dan acaba suka kai shi Filin Idi suka yanka shi, suka kuma fasa masa ciki hanji waje suka tafi. Ana cikin jimamin haka ne sai aka samu gawar wani mahauci a bayan gari a kan Titin Baifas, sai kuma wani yaro da aka kashe a Hayin Malam Sani da aka ce wa shi ramuwar gayya aka yi a kansa. Sai kuma wani da aka sare wa hannu aka cire masa amma bai mutu ba.
Sauran wadanda ’yan Sara-Sukan suka hallaka sun hada da wani mutum da aka kashe suka kuma aka datse masa hannuwa a Bakin Gulbi, lamarin kashe-kashen yana sanya jama’a shigewa gida bayan Sallar Magariba.
Malam Muhammad Adamu wani mazaunin garin Gusau ya bayyana wa wakilinmu cewa abin yana ba su mamaki ganin ga jami’an tsaro suna fitowa da sababbin motoci suna zagaye a gari amma a ce sun kasa maganin wannan al’amari.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Zamfara, DSP Sanusi Amiru, ya bayyana wa wakilinmu cewa ba su da labarin wadannan kashe-kashe da suke faruwa, wadanda suke da labara a kansu guda biyu ne kawai kuma sun samu nasarar kama mutun biyu daga ciki, kuma suna ci gaba da bincike a kai, duk wanda suka samu da laifi za su gabatar da shi a gaban kotu don yanke masa hukunci.