’Yan Sara-suka sun kashe matashi a wajen kalangu
Yan sara-suka sun halaka wani matashi a ranar Asabar da ta wuce a Unguwar Hayin Malam Bello da ke Kaduna.Matashin wanda ba a san daga inda yake ba, wasu matasa ne suka sassare shi a lokacin da ya halarci wani bikin aure da aka yi a unguwar.A cewar, majiyarmu bayan matasan sun sare shi sai […]
Yan sara-suka sun halaka wani matashi a ranar Asabar da ta wuce a Unguwar Hayin Malam Bello da ke Kaduna.
Matashin wanda ba a san daga inda yake ba, wasu matasa ne suka sassare shi a lokacin da ya halarci wani bikin aure da aka yi a unguwar.
A cewar, majiyarmu bayan matasan sun sare shi sai suka tsere suka bar shi kwance cikin jini daga bisani dattawan unguwar suka shaida wa ’yan sanda wadanda suka dauke shi zuwa asibiti.
“Gaskiya sun ji masa rauni sosai kuma ga dukkan alamu ya rasu domin idanunsa biyu sun kade kuma duk kokarin da muka yi domin wanke masa su ko za su koma ya ci tura,” inji wani magidanci a unguwar.
Bayanai sun nunawa cewa wata mace a unguwar da halayenta da na ’ya’yanta suke damun mutanen unguwar ne ake zargi da tara matasan da suka yi wannan danyen aiki.
Majiyarmu ta ce duk kokarin da dattawan unguwar suka yi wajen hana ta tara matasa masu zaman banza ya ci tura. “Sai da mai unguwarmu ya same ta ya ce kada ta yi kalangu amma ta yi. Ga shi kuma abin ya jawo har an yi kisan kai. Gaskiya kamata ya yi hukuma ta dauki mataki a kan irin wadannan mutane,” inji wani matashi a unguwar.
Mai Unguwar Hayin Malam Bello, Alhaji Ibrahim Fage ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni ’yan sanda suka kama matar da ta hada bikin. “Tana tsare a hannun ’yan sanda kuma suna bincike a kan wannan lamari. Wannan biki da ta hada ta gayyato masu kalangu kuma matasa daga unguwanni daban-daban sun taru saboda ’yan mata daga nan sai fada ya tashi a tsakaninsu. Muna kokari wajen wayar da kan iyaye a wannan unguwa tamu su daina gayyato masu kade-kade a duk lokacin da ake wani sha’ani a gidajensu. Mun kuma riga mun ba da sanarwa a masallatan unguwa saboda wayar da kawunan ’yan uwanmu,” inji shi.
Shi ma da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya ce rundunarsu ta kama mutum biyu da ake zargi da aikata laifin. “Muna tsare da mutum biyu dangane da kisan kuma muna ci gaba da bincike,” inji shi ta wayar tarho.