… ’Yan Saudiyya sun kashe Naira biliyan 160 a hidimar sallah

Mutanen Saudiyya sun kashe kimanin Riyal biliyan 40 (daidai da Naira biliyan 160) a bikin Edil fitir, wato karamar sallah, a karshen azumin watan Ramadana. A cewar masana tattalin arziki, kamar yadda jaridar Okaz ta ruwaito a ranar Alhamis din da ta gaba., ’yan Saudiyya sun kashe Riyal biliyan 10 a wajen tafiye-tafiye, da biliyan […]

… ’Yan Saudiyya sun kashe Naira biliyan 160 a hidimar sallah
… ’Yan Saudiyya sun kashe Naira biliyan 160 a hidimar sallah

Mutanen Saudiyya sun kashe kimanin Riyal biliyan 40 (daidai da Naira biliyan 160) a bikin Edil fitir, wato karamar sallah, a karshen azumin watan Ramadana. A cewar masana tattalin arziki, kamar yadda jaridar Okaz ta ruwaito a ranar Alhamis din da ta gaba., ’yan Saudiyya sun kashe Riyal biliyan 10 a wajen tafiye-tafiye, da biliyan 10 a wajen shakatawa da kuma biliyan 10 a wajen sayen nama.
Masanan sun ce, an kashe biliyan takwas wajen sayen kayan kawa da alatun gida, inda aka kashe a kalla Riyal biliyan biyu wajen sayen alawa da cakula. Sai dai rahoton alkaluman kudi da Larabawan suka kashe, bai bayyana yadda aka yi da sauran biliyan 10 ba, amma dai ya tabbatar da cewa a daidai irin wannan lokacin, mafi karancin abin da iyalai ke kashewa shi ne Riyal din Saudiyya dubu 10 (Daidai da Naira dubu 40).
Yawan kashe kudi wajen sayen abinci da kayan makwalashe al’ada ce da aka san mutanen Saudiyya da ita, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe