’Yan shekara 6 na samun horon tuki a Dubai
An bullo da shirin horar da kananan yara ’yan shekara shida tukin mota, don su zama managartan direbobi masu kula da ka’idojin tuki, saboda kare hadura a Dubai da Arewacin masarautun da suka hadu, suka yi Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).An kaddamar da shirin horar da matuka motoci ’yan shekara shida ne a makarantar Horizon International […]
An bullo da shirin horar da kananan yara ’yan shekara shida tukin mota, don su zama managartan direbobi masu kula da ka’idojin tuki, saboda kare hadura a Dubai da Arewacin masarautun da suka hadu, suka yi Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
An kaddamar da shirin horar da matuka motoci ’yan shekara shida ne a makarantar Horizon International d ake Dubai, ranar Talatar da ta wuce.
Horon da ake bai wa yaran, ya hada da daura bel da kayyade gudu. Wadanda suka shiga horon, sun kai yara 80, wadanda shekarunsu ya kama daga uku zuwa shida. Ana koyar da su yadda za su kiyaye ka’idojin hanya, a horion da aka yi wa lakabin “Horar da gwaraza,” wanda kamfanin kera motoci na Audi ya dauki nauyi.
Bayan da aka yi wa yaran jawabin fadakarwa, aka ilimantar da su irin yadda alamomin hanya suke, sai kawai yaran suka dare kananan motocinsu, inda suka rika nuna yadda ake amfani da ilimin tuki da suka koya.
Wani daga cikin yara direbobin, Elijah Cruz-Jabier, ya bayyana wa jaridar Khaleej Times, cewa: “Abin da na fi sha’awa, shi ne, in bugi bayan sauran motoci.” Sai dai da malaminsa ya yi tambaya, kan ko haka ya kamata mutane su yi a lokacin da suke tuki, ya amsa da cewa, “a’a.”
Da aka kammala horon, sai yara direbobin suka karbi lasisin tukinsu na “gwaraza.”
Hada wasannin nishadi da fadakarwar ilimin kare hadari a lokacin tuki, ya yi tasiri wajen nusar da yara muhimman darasi. A farkon bana ne, Ma’aikatar Harkokin cikin gida ta kasar ta bayar da sanarwar mutuwar mutum 55 da hadurra suka rutsa da su, kuma shekarunsu sun kama daga 18 zuwa sama a shekarar 2014.
Su kuwa jami’an kula da bin ka’idojin hanya, sun kawo rahoton cewa kananan yara 572 suka samu raunuka a hadurra 148 da aka yi a bara. A daukacin fadin kasar mutuwar kananan yara ta dauki kashi 7.7 cikin 100 daga cikin mutum 712 da suka rasu a hadurran mota.