’Yan Shi’a sun bukaci Najeriya ta yanke alaka da Isra’ila

Kungiyar ta ce abin da Isra’ila ke yi ta’addanci ne

’Yan Shi’a sun bukaci Najeriya ta yanke alaka da Isra’ila

‘Yan Shi’a

Kungiyar ’Yan Uwa Musulmai ta Najeriya (IMN) ta mabiya Shi’a ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta yanke alaka da kasar Isra’ila saboda yadda take kai hare-hare a kan Falasdinawa a Zirin Gaza.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Asabar, shugaban wani zaure na kungiyar, Farfesa Abdullahi Danladi, ya yi alla-wadai da ci gaba da hare-haren da ake kai wa Falasdinawan wadanda ya bayyana da na ta’addanci.

A cewarsa, “Makasudin taruwarmu a nan shi ne don mu yi muku bayani da ma mutanen Najeriya kan ci gaba da ayyukan ta’addanci da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi wa Falasdinawa.

“Kowa ya san yadda jagoranmu, Sheikh Ibrahim Yaqoub El-Zakzaky (H) yake fafutukar kare hakkin ba wai kawai Falasdinawa ba, har ma dukkan wadanda ake aikata wa danniya a fadin duniya.

“Abubuwan da suke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya a ’yan kwanakin nan, musamman a yankin Falasdinawa da aka mamaye, ya sake bude sabon shafi a tarihin dan Adam.

“A tsawon sama da shekara 75, Yahudawa sun rika kashewa tare da fitar da Falasdinawa daga gidajensu ta karfin tsiya, bisa goyon bayan ’yar korarsu, Amurka da sauran shaidanun kawayenta.

“Ya zuwa yanzu, an kashe dubban mutane, galibinsu mata da kananan yara. Wadannan hare-haren ba su kyale hatta asibitoci, makarantu, wuraren ibada ko ma sansanonin ‘yan gudun hijira ba.

“Ga wadanda ba su fahimci tarihi ba, suna ganin abin na da alaka da addini. Amma yadda suke tarwatsa hatta coci-coci, hakan na nuna duk lamarin ya wuce nan, aikin ta’addanci ne kawai a kan mutane.

“A kan haka ne muke kira da Gwamnatin Najeriya da ta gaggauta katse dukkan wata alakar da take yi da haramtacciyar kasar Isra’ila,” in ji shi.