’Yan Shi’a sun kai Buhari da sarakunan Kano da Zazzau da shugabannin Izala Kotun Duniya

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta ’yan Shi’a mai suna Islamic Human Rights Commission (IHRC) da ke kasar Ingilam, ta kai Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da Babban Hafsan Sojin kasar nan Laftana Janar Tukur Buratai, gaban Kotun Duniya tana neman a tuhume su da laifin kisan gilla […]

’Yan Shi’a sun kai Buhari da sarakunan Kano da Zazzau da shugabannin Izala Kotun Duniya

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta ’yan Shi’a mai suna Islamic Human Rights Commission (IHRC) da ke kasar Ingilam, ta kai Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da Babban Hafsan Sojin kasar nan Laftana Janar Tukur Buratai, gaban Kotun Duniya tana neman a tuhume su da laifin kisan gilla ga kisan ’ya’yan kungiyar Harkar Musulunci ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky a ranakun 12 da 14 ga Disamban bara.
Jaridar Premium Times da ake bugawa a Intanet wadda ta ruwaito jerin wadanda ’yan Shi’an ke son a hukunta ta ce kungiyar ta ’yan Shi’a ta kuma bukaci Kotun Duniyar ta tuhumi Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, kan tauye hakki da cin zarafin dan Adam game da kisan akalla mutum dubu mabiya Zakzaky.
kungiyar ta IHRC ta kuma kai karar shugabannin Izala da suka hada da Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir da Mataimakinsa Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun da Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakatarenta Sheikh Kabir Gombe da wani fitaccen malamin jami’a marubuci kan akidojin Shi’a, Farfesa Umar Labdo, inda su ma take nema Kotun Duniyar ta tuhume su kan cin zarafin dan Adam.
Sauran wadanda kungiyar ta IHRC take nema Kotun Duniyar ta tuhuma kan zargin hannunsu a kisan sun hada da Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman da Kwamandan Runduna ta daya da ke Kaduna Manjo Janar Adeniyi Oyebade da Kwamndan Daffon Sojoji na Zariya da Babban Hafsan Tsaro na Najeriya Laftana Janar Abayomi Olonisakin da Daraktan Kula da Harkokin Sirrri na Soji  da Babban Hafsan Sojin Leken Asiri Iya Bayis Mashal Riku Morgan da AK Ibrahim – Kwamnadan Rundunar Garisan ta daya da ke Kaduna da kuma Kanar F.M Babayo da Kyaftin Ben Ajatan na Daffon Sojin Najeriya.
A cikin bayaninta kungiyar IHRC ta ce harin da sojoji suka kai kan ’ya’yan kungiyar Shi’a ta IMN a ranakun 12 da 14 ga Disamba a Zariya ya kai na laifin cin zarafin dan Adam don haka tana kira ga Kotun Duniyar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin. “Ya kamata mai gabatar da kara na Kotun Duniya ya fara duba abin da ya auku a ranakun 12 da 14 ga Disamban bara a Zariya da ke Jihar Kaduna,” inji kungiyar IHRC.
kungiyar IHRC, ta bukaci Kotun Duniyar ta fadada sanya idonta kan harkokin Najeriya da sanya hannun sojoji a harin da aka kai ga ’yan Shi’a kuma mai gabatar da kara na kotun ya fitar da bayanin yin kandagarki na yana lura da rikicin na Najeriya kuma yana sane da aikata mugun laifi tare da gargadi ga wadanda suka yi laifin cewa za a hukunta su.
kungiyar ta ce kisan na Zariya ya cika sharudda biyu da suke sa a gabatar da batu a gaban Kotun Duniya don daukar matakin bincike kan cin zarafin dan Adam.
Tun a ranar Litinin ’yan Shi’a mabiya Zakzaky suka bayyana wa duniya cewa sun kai karar Gwamnatin Tarayya da sojoji zuwa Kotun Duniya a wani taron manema labarai da Kakakin kungiyar, Ibrahim Musa ya kira, inda ya ce sun garzaya kotun ce domin samun adalci.
Ya ce ce yadda abubuwa ke tafiya tun kama shugabansu ba su ga alamar samun adalci daga hannun Gwamnatin Tarayya ba abisa kisan kiyashi da aka yi musu a Zariya.
“Saboda haka muka ga ya dace mu shigar da kara a Kotun Duniya domin a yi mana adalci. A cikin wannan kasa ne aka kashe mutum sama da dubu daya a Zariya cikin kwana biyu. Sannan da yawa suna tsare a gidajen yari ba tare da an sake su ba domin zuwa neman magani. Shugabanmu Ibrahim Zakzaky da matarsa duk an harbe su kafin a tafi da su. Kuma a yau sun wuce kwana 100 a hannun jami’an tsaro. Duk kokarin da lauyoyinmu suka yi na ganinsa a hedkwatar Hukumar Tsaro (DSS) a Abuja ya ci tura. Saboda haka mun san an take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa kuma dan Adam,” inji shi.
Wata kungiyar ’yan Najeriya mazauna kasashen waje da ake kira The Nigerians in Diaspora Monitoring Group (Reshen Ingila) ta yi barazanar gurfanar da kungiyar IHRC a gaban Kotun Duniyar ita ma kan abin da ta kira bata sunan sojojin Najeriya a rahotonta kan rikicin ’yan Shi’a  da sojoji a Zariya.
Wakilin kungiyar na Ingila, Adeka Onyilo ya fadi a wata sanarwa cewa ’yan Najeriya masu kishinta ba za su zauna su zuba ido ba a lokacin da kungiyar IHRC take bata sunan sojojin Najeriya da tozarta Gwamnatin Tarayya ba ta wajen ingiza wasu suna karya doka da oda ba.
kungiyar ta ce ta ji mamaki kan yadda a lokacin da ’yan Shi’a suke gallaza wa mutanen Zariya da karya doka bisa gadara da yin tawaye wa hukumomi da kuma yadda ’yan Boko Haram suka yi ta kashe dubban mutanen Najeriya, amma ko kala kungiyar IHRC ba ta ce a kai ba, balle ta la’anci hakan.
“Mu ’yan Najeriya mazauna kasashen waje muna mamaki kan yadda wannan kungiya mai suna IHRC ta tsuke bakinta a tsawon shekarun da Boko Haram suke karkashe mutane, wadda bangaren soji ne na Harkar Musulunci, kuma ko da ziyartar iyalan da ke sansanonin ’yan gudun hijira ba ta yi ba, balle ta bayar da tallafi ga marasa gidaje da marasa lafiya da masu neman taimako daga cikinsu. Don haka ’yan Najeriya mazauna kasahen waje za su kalubalance su da masu goya musu baya a gaban Kotun Duniya domin duniya ta san gaskiya kuma kada ta goyi bayan hadin bakin zalunci don bata sunan Najeriya.”