’Yan sintiri sun kama ’yan Boko Haram a Maiduguri *Boko Haram sun hallaka sama da mutum 100 a Yobe
Rahotanni daga Maiduguri fadar Jihar Borno sun ce ’yan sintiri da aka fi sani da Sibiliyan JTF sun kama wasu mutum hudu da ake zargin ’yan Boko Haram ne a lokacin da suke kokarin shiga birnin.Wata majiya da ba ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa gidan rediyon BBC cewa a yammacin shekaranjiya Laraba […]
Rahotanni daga Maiduguri fadar Jihar Borno sun ce ’yan sintiri da aka fi sani da Sibiliyan JTF sun kama wasu mutum hudu da ake zargin ’yan Boko Haram ne a lokacin da suke kokarin shiga birnin.
Wata majiya da ba ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa gidan rediyon BBC cewa a yammacin shekaranjiya Laraba ne ’yan sintirin suka kama mutanen a kan hanyarsu ta shiga Maiduguri daga garin Dikwa.
Ana tsammanin luguden wutar da sojoji ke yi ga ’yan kungiyar ne ya sa suke neman barin maboyarsu.
Wata majiya ta ce ’yan sintirin sun mika mutanen ga sojojin Sector 2 da ke Maiduguri.
A wani labarin, wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne a karo na biyu cikin mako biyu sun sake kai kazamin hari a kauyen Kukuwa Tasha a karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, inda ake zargin sun hallaka sama da mutum 100 da akasarinsu yara ne.
Wani mazaunin Kukuwa Tasha da ya sha da kyar kuma ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, maharan Boko Haram a wannan karon sun shiga garin ne da misalin karfe 7:30 na yamma, lokacin da ake haramar Sallar Isha’i ana cikin ruwan sama.
Ya ce lokaci guda maharan suka fara harbe-harben kan mai uwa da wabi, inda mutane suka shiga guje-guje tare da rugawa daji.
Ya ce, duk da ruwan da ake shekawa a daji suka kwana sai da gari ya waye ne suka dawo suka tarar da aika-aikar da ’yan ta’addan inda suka iske gawarwaki sama da mutum 100 suka yi jana’izarsu.
Da Aminiya ta tuntubi kansilan Kukuwa, Malam Nuhu Baba Ambiya, ya ce sun samu labarin aukuwar haka amma suna kokarin bincikar lamarin.
Sai dai Kakakin Rundunar Soji Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya ce, rundunarsu ba ta tabbatar da faruwar harin da ake fada ba, sai dai suna bincike don gano gaskiyar lamarin, amma akwai tababa kan hakan.