’Yan sintiri sun lashi takobin ganin ba a sake rikici a Filato ba
Mataimakin Kwamandan kungiyar ’Yan sintiri ta Najeriya a Shiyyar Arewa ta Tsakiya, Alhaji Garba Juji ya ce kungiyarsu ta lashi takobin ganin ba a sake samun wani rikici ba a Jihar Filato. Alhaji Garga Juji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce a halin yanzu suna […]
Mataimakin Kwamandan kungiyar ’Yan sintiri ta Najeriya a Shiyyar Arewa ta Tsakiya, Alhaji Garba Juji ya ce kungiyarsu ta lashi takobin ganin ba a sake samun wani rikici ba a Jihar Filato.
Alhaji Garga Juji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce a halin yanzu suna tura mutanenmu wasu a kayan sarki wasu a farin kaya zuwa wuraren ibada na Musulmi da Kirista da kasuwanni da tashoshin mota a jihar don gadin wuraren.
Ya ce duk wanda suka gani a irin wadannan wurare idan ba su yarda da shi ba, za su iya kama shi su mika wa ’yan sanda.
Ya ce, “A wannan aiki da muke yi duk shugabannin ’yan sanda na kananan hukumomin jihar nan da shugabannin rundunar tsaro ta musamman (STF) suna ba mu goyon baya da hadin kai.”
Ya ce kungiyar ’yan sintiri hade take a jihar, ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, domin akwai dukkan kabilun da ke jihar a cikin kungiyar.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta sanya shugabannin kananan hukumomi su rika tallafa wa kungiyar a kananan hukumomi da motocin sintiri da kayan aiki. Ya ce idan aka tallafa wa ’yan sintiri za su magance matsalar batagarin da suke damun al’umma a jihar.
Daga nan ya yi kira ga ’yan kungiyar kan su guji daukar doka da oda a hanunsu