‘Yan siyasa 39 sun zama jakadun Najeriya
Majalisar Dattawa ta amince shugaban kasa Buhari ya nada wasu mutum 39 da ya gabatar mata da sunayensu a matsayin sabbin jakadun Najeriya. Amincewar Majliar ya biyo bayan karbar rahoton kwamitinta na kasashen ketare da ya tantance karkashin Sanata Adamu Bulkachuwa wanda za a nada din. Shugaba Kwamitin ya ce an dage amincewa da nadin […]
Majalisar Dattawa ta amince shugaban kasa Buhari ya nada wasu mutum 39 da ya gabatar mata da sunayensu a matsayin sabbin jakadun Najeriya.
Amincewar Majliar ya biyo bayan karbar rahoton kwamitinta na kasashen ketare da ya tantance karkashin Sanata Adamu Bulkachuwa wanda za a nada din.
Shugaba Kwamitin ya ce an dage amincewa da nadin jakadu daga jihohin Yobe da Neja, saboda da rikicin da ya dabaibaye mika sunayensu.
Zaman majalisar na ranar Laraba ya kuma amince Shugaba Buhari ya nada Suleiman Sani a matsayin kajada daga birnin tarayya.
Sanata Philip Aduda mai wakilatar Birnin Tarayya ya koka cewa babu dan mazabarta a cikin jerin ‘yan siyarar da za a ba wa jakadanci.
Amma Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan ya ce “za ku samu domin ba a rufe mika sunayen wandanda za su zama jakadu ba”.
Sai dai ya yi kira ga Gwamantin Tarayya da ta samar wa ofisoshin jakadancin Najeriya isassun kudaden gudanarwa.
Ya ce babu amfanin tura mutum wakiltar kasarsa a wata kasa amma a kyale shi da rashim muhimman bukatunsa na gudanar a aikin da aka ba shi.
Idan ba za a wadatar da su ba kudade ba to gara a rage yawansu, inji shi.