’Yan siyasa ba sa martaba sarautar gargajiya – Sarkin Suleja
Mai martaba Sarkin Suleja Alhaji Muhammadu Awwal Ibrahim ya cika shekara 20 a bisa karagar mulkin Suleja. Alhaji Awwal Ibrahim wanda ya zama gwamnan jihar Neja a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983,an nada shi a matsayin sarkin Suleja ne a shekarar 1993. Aminiya ta tattauna da shi inda ya yi bayani a kan al’amura da […]
Mai martaba Sarkin Suleja Alhaji Muhammadu Awwal Ibrahim ya cika shekara 20 a bisa karagar mulkin Suleja. Alhaji Awwal Ibrahim wanda ya zama gwamnan jihar Neja a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983,an nada shi a matsayin sarkin Suleja ne a shekarar 1993. Aminiya ta tattauna da shi inda ya yi bayani a kan al’amura da dama. Ga yadda hirar ta kasance.
Aminiya: Ga shi yanzu ka cika shekara 20 a bisa karagar mulikin masarautar Suleja, ko za ka bayyana mana tarihin masarautar a takaice?
Mai martaba Sarki: Ina godiya ga Sarki Allah. A takaice dai an kirkiro masarautar Suleja ne kusan shekaru 200 da suka gabata, a wancan lokacin tana cikin yankin kudancin masarautar Zazzau ne.Sarkin Habe na karshe da ya yi sarauta kafin Fulani mallawa, shi ne ya ga ya dace ya zauna a nan tare da jama’arsa lokacin da Fulani masu jihadi suka kore shi daga Zariya. Lokacin da ya fito ya zo nan ya zauna a wurare da dama a yankin da a wancan lokacin ake kira kudancin masarautar Zazzau. A karshe sai ya zauna a Zuba. A lokacin da yake kokarin fadada mulkinsa ya yi yake-yake da al’ummomi da dama. Kamar yadda tarihi ya nuna an ce ya rasa ransa ne a wuraren Lapai. Kafin ya rasu ya bar wasiyar cewa jama’arsa su rungumi dan uwansa Abu-ja a matsayin shugaban al’ummar zage-zagi na wancan lokacin. Domin haka Abu-ja shi ne ya kafa Suleja ta yanzu, wanda a da ake kiranta Abuja, watau aka sanya wa garin sunansa.
Bayan ya rasu sai dan uwansa Abu-kwakwa, wanda dan uwa ne shakiki ga Makau sarkin habe na Zazzau na karshe, ya gaje shi. Ta haka ne aka samu gidajen sarauta guda biyu a Suleja kuma ake ta amfani da su har zuwa yau da na shekara 20 a kan karagar sarautar Suleja.
Kamar yadda kuka sani ne, an kafa wannan wuri ne saboda tasirinsa a lokacin yaki, domin garin yana wani kwazazzabo mai kewaye da tsaunuka da ke taimakawa wajen yaki. Tun a wancan lokacin garin ya rika tattara kabilu daban-daban wadanda kafin kafuwar garin suke karkashin tsohuwar masarautar Zazzau.
Tun kafuwar masarautar Suleja an yi sarakunan guda bakwai, nine na takwas a jerin sarakunan, kuma Fulani masu jihadi ba su taba cin Suleja da yaki ba, haka su ma turawan mulkin mallaka, Sarki Ibrahim shi ne ya yi fada da turawa har sai da ya rasa ransa. Kakana Mamman Gani shi ne ya gaje shi.
Turawan mulkin mallaka a lokacin sun zargi mutanenmu da cewa fitinannu ne da suke yi wa ‘yan kasuwa masu safara tsakanin kudanci da arewacin kasar nan kwanton-bauna.
Aminiya: Yaya aka yi garin Suleja ya canja zuwa cibiyar kasuwanci kamar yadda yake a yau?
Mai martaba Sarki: Hakan ya faru ne saboda rungumar jama’a da sarakunan kasar suka yi, musamman Sarki Suleiman Barau, wanda shi ne sarki na farko da ya samu ilimin boko. Ya jawo mutane iri-iri domin su zauna a garin,tare da karfafa gina makarantu, wanda ya karfafa wa mutane, musamman yarbawa daga Ogbomosho suka zo su zauna a nan, mafi yawan wadannan mutanen ‘yan kasuwa ne.
Garin Suleja ya kasura ya zama cibiyar kasuwanci ne a karshen zamanin marigayi Sarki Ibrahim Dodo Musa wanda na gada. A wancan lokacin ne gwamnatin tarayya ta yanke shawarar canja hedkwatar kasar nan daga Legas zuwa Abuja, a lokacin ni ma’aikacin gwamnati ne da ke da matsayin babban sakatare a gwamnatin jihar Neja. Wannan ne ya sanya mutane suka yi ta kwararowa suna zuwa su zauna a nan. Wannan babban cigaba ne, amma yana da nasa illolin, domin ya zama matattarar mabarnata, musamman dinbin matasan da ba su da aikin yi, domin matsalar tsaro da rikicin filaye su ne suke ci mana tuwo a kwarya.
Aminiya: Ka yi bayanin matsalolin da ke faruwa a tsakanin jama’a, matsalolin da ke shafar yanayi da kuma rashin cigaba fa?
Mai martaba Sarki: Ba a bai wa garin muhimmancin da ya kamata saboda taimaka wa Abuja da yake yi, kuma na yi bayanin matsalar da tururuwar jama’a ta jawo mana, duk wadannan sun taimaka wajen lalacewar muhalli da rashin tsarin gari da talauci da kuma jahilci a tsakanin jama’armu. A sakamakon haka za ka ga mutane suna kokarin rayuwa ta kowane hali, ko dai ta hanyar sayar da filayensu, duk da shawarar da muke ba su su guji yin hakan, ko kuma su rika aikata miyagun laifuffuka kamar garkuwa da mutane da sauransu. Mutane, musamman matasa suna amfani da girman da garin Suleja yake da shi su rika yin abubuwan da ke gurgunta cigaban garin Suleja. Kwanan nan muka nuna damuwarmu game da yadda wata gunduma a masarautar ta zama cibiyar aikata barna iri-iri kuma muka yi sa’a aka magance matsalar.
Muna fuskantar matsaloli iri-iri, na fahimci cewa garin Suleja matattarar dimbin makarantu masu zaman kansu ce, amma wadansu daga cikinsu ba masu inganci ba ne. Saboda ba a tsara garin yadda zai zama mai taimaka wa Abuja ba shi ya sanya muke fuskantar matsala. Duk wani kokarin za a yi ba za a ganinsa kuru-kuru ba saboda ba mu da kyakkyawan tsarin gari.
Aminiya: Mene ne dangantakar Suleja da jihar Neja inda garin yake karkashinsa yanzu?
‘Yan siyasa sun yi watsi da masarautar Suleja, mun sha bayyana wa shugabannin siyasa cewa mu ba ‘yan hamayya ba ne, kamar yadda ake kuskuren daukarmu. Masarautar Suleja tana kunshe ne da kwararrun mutane masu hangen nesa, amma abin takaici ba mu samun fahimta da goyon baya daga shugabannin siyasarmu, domin haka muke samun matsala.
Aminiya: Yaya za ka bayyana halin da sarautar gargajiya yake ciki yanzu da kuma yadda yake a baya?
Mai martaba Sarki: Wannan tambaya ce mai wuyar amsawa a gare ni, domin na san kokarin da manyan sarakuna suke yi domin gwamnati ta fahimci rawar da sarakuna suke takawa, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya da wayar da kan jama’a, domin ta samar musu da matsayi a tsarin mulkin kasar nan.Ina fatan za su cimma nasara. Amma ni a ganina shugabannin siyasa ba su bai wa sarauta matsayi da martabar da suka kamace ta, suna amfani da sarakuna ne kawai idan wata matsala ta taso ana neman su yi maganinta. Domin haka duk wanda ya yarda cewa muna taikamawa wajen wanzar da zaman lafiya, duk da matsanancin talauci da jahilci da cututtukan da ke addabar jama’a, ya kamata ya yaba ya kuma bayar da gudunmuwarsa wajen cimma wannan burin.
Aminiya:Yanzu da ka cika shekara 20 a karagar mulki wane sako kake da shi ga jama’arka?
Mai martaba Sarki: Abin da na fi kauna shi ne garin Suleja ya ci gaba da zama wurin da duk wanda ya zo ya zauna tare da mu zai samu kwanciyar hankali. Sai dai kuma ya kamata irin wadannan mutanen su fahimce mu, su girmama al’adunmu, su hada kai da mu. Amma idan burinsu shi ne su zo su kwace mana filayenmu ba za mu yarda ba, domin na yi imanin cewa mun bayar da duk gudunmuwar da ta kamata ta hanyar bayar da filayenmu domin a gina sabuwar hedkwatar kasar nan. Saboda haka duk wanda yake son ya zo ya zauna tare da mu dole ne ya girmama al’adunmu ya kuma ba mu cikakken hadin kai. Ba za mu nuna wa kowa bambanci ba. Kuma ina kira ga jama’ata su ci gaba da hakuri da junansu tare da rungumar duk wanda ya zo ya ce zai zauna tare da su, amma kuma su kula da tsaron yankinsu, su kuma kare mutuncinsu, kada su bayar da kafa ga duk wani wanda zai nemi zubar musu da mutunci.