‘Yan Siyasa: Dole ne a daina sayen ƙuri’u – Abdulsalami

Abdulsalami ya buƙaci ‘yan takarar gwamna da su amince da sakamakon zaɓen matuƙar an yi zaɓe cikin gaskiya

‘Yan Siyasa: Dole ne a daina sayen ƙuri’u – Abdulsalami

Tsohon shugaban Nijeriya na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya buƙaci ‘yan siyasa da su kawo ƙarshen salon sayen ƙuri’u.

Abdulsalami, wanda shi ne Shugaban Kwamitin zaman lafiya na ƙasa (NPC), ya bayyana hakan a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

An gudanar da taron yarjejeniyar ne a Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a. Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan takarar jam’iyyun siyasa 17 da suka shiga zaɓen sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Abdulsalami ya buƙaci ‘yan takarar gwamna da su amince da sakamakon zaɓen matuƙar an yi zaɓe cikin gaskiya da aminci.

Ya ce duk ‘yan takarar da ke ganin bai gamsu da sakamakon zaɓen ba zai iya neman halaltacciyar hanya ta zaman lafiya don gabatar da ita kan wata damuwa da ka iya tasowa bayan zaɓen.

“Ina kira ga duk ‘yan siyasar da za su rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da su bai wa kansu da jam’iyyunsu cikakku kan yarjejeniyar da su ƙaurace wa tashe-tashen hankula da tsoratarwa, su kuma tuna cewa a matsayinku na ‘yan siyasa, dole ne ku nuna halin kishin ƙasa domin wannan shi ne  kyakkyawan hali na shugabanci,” in ji shi.

“Ya zama haƙƙi na ‘yan Nijeriya su zaɓi shugabanninsu ba tare da nuna son kai ba. ’Yan siyasa su daina barazana ta cinikin ƙuri’u.”

A yayin da yake yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bisa ayyukan da ta gudanar ya zuwa yanzu, Abdulsalami ya roƙi hukumar zaɓe da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da cewa masu kaɗ a ƙuri’a sun gudanar da zaɓensu cikin lumana.