’Yan siyasa ke ruruta rikicin kabilanci – Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya dora alhakin ruruwar rikicin kabilanci a kan ’yan siyasa da ke son cimma bukatunsu na son rai. Sarkin Musulmi ya yi ikirarin ne a cocin Saint Dabid’s Cathedral da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata, a wurin taron kwana biyu da […]
LONDON, ENGLAND – FEBRUARY 18: The Sultan of Sokoto, Mohamed Sa’ad Abubakar waits to meet Prince Charles, the Prince of Wales at Clarence House on February 18, 2009 in London. The Sultan is the titular ruler of Sokoto in northern Nigeria. He is the leader of approximately 70 million Nigerian and West African Muslims and […]
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya dora alhakin ruruwar rikicin kabilanci a kan ’yan siyasa da ke son cimma bukatunsu na son rai.
Sarkin Musulmi ya yi ikirarin ne a cocin Saint Dabid’s Cathedral da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata, a wurin taron kwana biyu da Cibiyar Tuntuba Tsakanin Addinai (NIREC), ta shirya.
Ya shawararci ’yan Najeriya sun kaurace wa ’yan siyasa da masu hannu da shuni da ke tsoma rigar siyasa a harkokin addini.
Ya ce Alkur’ani Mai girma da Baibul ba su da alaka da kowace jam’iyya.
Dangane da rushe masallaci a Fatakwal da ake zargin gwamnatin Jihar Ribas da yi, ya ce tuni NIREC a matsayinta na uwa a kasa ta dauki alhakin lalubo hanyar samar da maslaha.
Sarkin Akure (Deji na Akure) Oba Aladetoyinbo Aladelusi ne gayyaci Sarkin Musulmi domin halartar taron da ake gudanarwa a kowace shekara don inganta al’adu.