’Yan siyasa ku tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe – Janar Abdulsalami

Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Kasa a lokutan zabe, kuma tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdussalam Abubakar (ritaya) ya shawarci ’yan siyasa su tabbatar sun zauna lafiya da junansu musamman a lokacn zabe da ke tafe. Tsohon Shugaban Kasar ya yi wannan kira ne lokacin taron sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a […]

’Yan siyasa ku tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe – Janar Abdulsalami
’Yan siyasa ku tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe – Janar Abdulsalami

Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Kasa a lokutan zabe, kuma tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdussalam Abubakar (ritaya) ya shawarci ’yan siyasa su tabbatar sun zauna lafiya da junansu musamman a lokacn zabe da ke tafe.

Tsohon Shugaban Kasar ya yi wannan kira ne lokacin taron sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ’yan takarar Gwamnan Jihar  Kano da aka gudanar a gaban jami’an Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu  kan zabe.

Shugaban ya  ce babu kasar da za ta ci gaba idan babu zaman lafiya don haka ya yi kira ga al’ummar kasar nan gaba daya su rungumi dabi’ar zaman lafiya, ba wai sai a lokacin zabe ba.

A jawabin Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya ja hankalin jagororin siyasa a dukan matakai su sa magoya bayansu su daina yawo da makamai a lokacin yakin neman zabe. “Yawo da makamai da matasa ke yi a lokacin yakin neman zabe ba abu ne da zai haifar da da mai ido ba. Don haka akwai bukatar a ja hankalin matasanmu su ajiye makamai,” inji shi.

Sarkin ya yi kira ga ’yan takara su karbi sakamakon zabe da zuciya daya ko sun yi nasara ko kuma sun fadi.

Kimanin ’yan takarar kujerar Gwanman Jihar 21 ne suka sanya hannu a kan yarjejeniyar, inda suka sha alwashin wanzar da zaman lafiya a lokacin zabe mai zuwa da kuma bayansa.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta