Yan siyasa na rububin nema wa ’yan takararsu mukamai

Wata majiya ta tseguntawa Aminiya cewa manyan ’yan siyasa da masu fada-a-ji sun fara shirye-shiryen tura ’yan takararsu gaba-gaba yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin fadada majalisar ministocinsa. Shugaba Muhammadu Buhari a taron shugabannin jam’iyyar APC a makon da ya gabata ya bayyana aniyarsa na fadada majalisar ministocinsa. Majiyar daga majalisar dokoki da kuma […]

Yan siyasa na rububin nema wa ’yan takararsu mukamai

Wata majiya ta tseguntawa Aminiya cewa manyan ’yan siyasa da masu fada-a-ji sun fara shirye-shiryen tura ’yan takararsu gaba-gaba yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin fadada majalisar ministocinsa.
Shugaba Muhammadu Buhari a taron shugabannin jam’iyyar APC a makon da ya gabata ya bayyana aniyarsa na fadada majalisar ministocinsa.
Majiyar daga majalisar dokoki da kuma fadar shugaban kasa ta bayyana cewa tuni aka fara mika sunayen don tantance su.