’Yan siyasa ne matsalar kasar nan – Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ’yan siyasa ne matsalar kasar nan, idan aka dubi yadda harkokin a tsaro ke dada tabarbarewa saboda karatiwar zaben 2015.Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a fadarsa yayin zantawa da manema labarai […]
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ’yan siyasa ne matsalar kasar nan, idan aka dubi yadda harkokin a tsaro ke dada tabarbarewa saboda karatiwar zaben 2015.
Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a fadarsa yayin zantawa da manema labarai da ya shirya wa buda-baki.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce sulhu tsakanin gwamnati da ’yan kungiyar Boko Haram shi ne mafita in ana son kubutar da ’yan matan Chibok da kawo karshen hare-haren da suke kaiwa, “Sasantawa na sa a samu nasara a kowane lamari shi ya sa na yarda da sulhu a cikin kowane lamari. Duk mutanen da ka ji suna fadar kada a yi sulhu da ’yan Boko haram, ba wadanda aka sace wa ’ya’yansu ba ne, in da ’ya’yansu ne ko nawa ake bukata na kudi za su bayar a mayar musu da su gida balle sulhu. Don ko kasar Amurka tana tuntubar mayakan Taliban da Alka’ida, kuma saboda Ba’amirke daya Shugaban Amurka ya saki manyan mayakan Taliban biyar da ake tsare da su a gidan kaso. Kuma ya saki ’yan Alka’ida biyar don kubutar rayuwar dan Amurka daya, to, don me ba za a yi haka a Najeriya ba,” inji Sarkin Musulmi.
Ya ce ba wata kasa da za ta ci gaba a duniya ta hanyar aikata rashin gaskiya, “Wasu na cewa mu jagororin addini ba mu yin abin da ya kamata mu yi, bayan muna sukar zalunci kuma ba mu yarda da shi ba, to me suke son mu yi?,” ya tambaya.
Kan yin katin izinin zama a yankin Kudu maso Gabas da aka umarci ’yan Arewa da yi, Sarkin Musulmin ya nuna takaicinsa, inda ya ce ana so ne a lakaba wa mutanen Arewa jangwam ta nuna duk wanda ya fito daga yankin dan Boko Haram ne, kuma ya ce wannan babbar matsala ce ga ci gaban kasar nan kuma za ta iya haifar da matasala.
Buda-bakin ya samu halartar Bishop din Cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Hassan Kuka da lauyan mai rajin kare hakkin dan Adam, Mista Solomon Dalung da shugaban kungiyar Muryar Talaka ta kasa Zaidu Bala da sauran kungiyoyi da daidaikun jama’a.