’Yan siyasa su daina neman kuri’a da sunan Sardauna – Sarkin Hausawan Ile-Ife

Sarkin Hausawan Ile Ife, a Jihar Osun, Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali, ya bukaci ’yan siyasa su daina tallata kawunansu,  hanyar amfani da sunan Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello, don neman kuri’un talakawa, kamar yadda ya bayyana wa sashen Hausa na rediyon Muryar Amurka, a wata hira da aka yi da shi, ranar Asabar din makon […]

’Yan siyasa su daina neman kuri’a da sunan Sardauna – Sarkin Hausawan Ile-Ife
’Yan siyasa su daina neman kuri’a da sunan Sardauna – Sarkin Hausawan Ile-Ife

Sarkin Hausawa, Alhaji Abubakar Mamuda MadagaliSarkin Hausawan Ile Ife, a Jihar Osun, Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali, ya bukaci ’yan siyasa su daina tallata kawunansu,  hanyar amfani da sunan Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello, don neman kuri’un talakawa, kamar yadda ya bayyana wa sashen Hausa na rediyon Muryar Amurka, a wata hira da aka yi da shi, ranar Asabar din makon jiya.
“Idan har za su yi amfani da wannan fitaccen suna a duniya to, lallai ne suyi koyi da shi wajen tsoron Allah (SWT) da kwatanta gaskiya da adalci da kuma aikata abubuwan ci gaban jama’a a bayyane ba surutu da fatar baki ba,” inji shi.
Ya ce, muhimman ayyukan da marigayi  Sardaunan Sakkwato a zamanin mulkinsa sun hada da gina gidan Rediyon Najeriya na Kaduna da kafa Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da wadanda aka yi amfani da su wajen wayar da kan talakawa.  
“Dukkan wata kafar watsa labarai ta duniya dake amfani da harshen hausa wajen watsa shirye shiryenta, tana koyon Gidan Rediyo Najeriya na Kaduna da Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da Sardaunan Sakkwato, ya tabbatar da kafuwarsu a lokacinsa,  wadanda har yanzua miliyoyin al’ummar kasar nan suke cin moriyarsu.
A cewarsa, ba za a taba mantawa da irin wadannan muhimman ayyuka da Sardauna ya yi domin amfanin jama’arsa ba. Saboda haka muke so shugabanni da suke mulki a yanzu, su daina amfani da sunan Sardaunan Sakkwato da bakinsu, muna so ne su aikata irin ayyukan da ya gudanar a bayyane.”
Sarkin Hausawan ya jinjina wa gidan Rediyon Ameurka (bOA), kan sababbin shirye-shiryen da ya fito da su, inda masu sauraro ke mika koke-koke da shawarwarinsu kai tsaye, ba tare da matsala ba. Ya nemi wakilan Gidajen Rediyo na kasashen duniya da suke gudanar da ayyukansu a Najeriya, su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu tsakani da Allah.