’Yan siyasa sun yi wa Gwarazan Gasar Hikayata ta 2023 ruwan kudi
A’isha Adam Usaini ce gwarzuwar Hikayata ta 2023 da labarinta mai taken ‘Rina A Kaba’.
Manyan ’yan siyasa sun yi wa Gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023 ruwan kudi yayin da suka halarci bikin karramawar a Abuja.
A yammacin wannan Alhamis din ce dai aka gudanar da bikin karrama gwarazan gasar gajerun kagaggun labarai ta mata zalla da BBC Hausa ya saba gudanarwa duk shekara.
- Amira Souley: Tattaunawa da Gwarzuwar Hikayata ta 2022
- A Karon Farkon ’Yar Kasar Nijar Ta Lashe Gasar Hikayata
A’isha Adam Usaini ce gwarzuwar Hikayata ta 2023 da labarinta mai taken ‘Rina A Kaba’—wanda ya yi tsokaci a kan irin yadda mata ke amfani da magungunan mata, ba tare da la’akari da irin illar da ire-iren wadanan magunguna ke haifarwa ba.
A’isha Abdullahi Yabo ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna Bakin Kishi.
Sai kuma A’isha Sani Abdullahi daga birnin Jos na Jihar Filato da ta zo ta uku wadda ta rubuta labarin Tuwon Kasa.
Daga cikin manyan baki da suka halarcin bikin karrama wadannan gwaraza, akwai fitattun ’yan siyasa da suka gwangwaje wadannan mata sanadiyar bajintar da suka yi
Ga bayanin wasu daga cikin manyan bakin da suka bai wa gwarazan gasar bana kyautar kudi kamar yadda BBC ya tabbatar:
1. Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, uwargidan shugaban jam’iyyar APC na kasa ta bai wa:
a. Aisha Adam Usaini — $1,500
b. Aisha Abdullahi Yabo — $1,000
c. Aisha Sani Abdullahi — $500
2. Gwamna Kebbi Nasir Idris — N3,000,000
3. Sanata Tanko Al-Makura — N1,000,000
4. Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Umar Radda — N1,000,000
5. Sanata Abdul’aziz Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, kuma Sanatan Zamfara ta Yamma — N5,000,000
6. Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila — N500,000