’Yan siyasar Najeriya na neman mulki ne don arzurta kansu – Ambasada Hans

Jakadan kasar Swizland a Najeriya Dokta Hans Rodulf Hodel ya ce ba wata hanya da za a bi domin a samu ci gaban kasa illa kasar nan ta yi da gaske wajen inganta ilimi.Ambasada Hans ya bayyana haka ne lokacin da ya halarci wata tattaunawa ta ’yan jarida da dalibai da kuma ma’aikatar Jami’ar Amurka […]

’Yan siyasar Najeriya na neman mulki ne don arzurta kansu – Ambasada Hans
’Yan siyasar Najeriya na neman mulki ne don arzurta kansu – Ambasada Hans

Jakadan kasar Swizland a Najeriya Dokta Hans Rodulf Hodel ya ce ba wata hanya da za a bi domin a samu ci gaban kasa illa kasar nan ta yi da gaske wajen inganta ilimi.
Ambasada Hans ya bayyana haka ne lokacin da ya halarci wata tattaunawa ta ’yan jarida da dalibai da kuma ma’aikatar Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) da ke Yola.
Dokta Hans ya ce za a iya magance matsalar tsaro a kasar nan in mutane suka samu ilimi da kwarewa a fannoni ilimi da kere-kere.
Ya ce kasarsa na tafiyar da harkar gwamnati kamar na Najeriya sai dai bambancin shi ne shekarun da masu mulki suke yi a gwamnati daban ne da nasu.
Ya ce “Da hukumomin gwamnati manya da kanana muna da ministoci bakwai ne da Shugaban kasa da zai yi shugabanci na shekara daya. Siyasar kasarmu na mutane ne da suke kokarin yi wa mutane aiki, amma a kasashe masu tasowa irin Najeriya, ’yan siyasa na neman shugabanci ne ba don komai ba, sai domin su azurta kansu.”
Ya ce a kowace kungiya ko jam’iyya bakwai da suke da su, a kowadanne shekara hudu, mutum daya daga cikin kowace jam’iyya ake nadawa ya yi shugabanci.
Dokta Hans ya ce, sun kulla yarjejeniyar tare da Najeriya a harkar yawon shakatawa da kuma kasuwanci. Ya ce kasarsu Switzerland na da kamfanoni 600 a Najeriya. Ya kuma ba da shawarar kan yadda za a magance matsalar tsaro, inda ya ce a zauna a kulla yarjejeniyar zaman lafiya da masu tayar da kayar baya.