’Yan siyasar yau ba su da akida – Sanata Sani
Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce mafi yawan ’yan siyasar kasar nan ba su da akida. A cewarsa, akwai bukatar ’yan siyasa su zamo masu siyasar akida a kasar nan. Sanata Shehu Sani ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Balarabe […]
Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce mafi yawan ’yan siyasar kasar nan ba su da akida. A cewarsa, akwai bukatar ’yan siyasa su zamo masu siyasar akida a kasar nan.
Sanata Shehu Sani ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa a ranar Lahadin da ta gabata a Kaduna.
Ya bayyana Alhaji Balarabe Musa a matsayin jagoransa kuma abin koyi a siyasar kasar nan saboda akidarsa ta siyasa da tausayin talakawa.
Sanata Shehu Sani ya ce dole ne ’yan siyasar gaskiya su zamanto masu siyasar akida kamar Alhaji Balarabe Musa in dai da gaske siyasar suke yi.
“Na zo nan gidan ne domin in gana da jagorana kuma abin koyi gare ni a siyasance, wato Alhaji Balarabe Musa saboda tausayinsa ga talaka da kuma irin gwagwarmayar da ya yi domin ci gaban siyasar kasar nan. Ga shi kuma abin da muka rasa a siyasarmu ta yau ke nan domin akasarin ’yan siyasar yau ba su da akida. Kuma ya kamata a ce muna da akida kamar ta su Malam Balarabe Musa,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Muna murna da irin gudunmawar da ya bayar wajen kwatar wa talakawa ’yancinsu da kuma kasar nan. Abin koyi ne gare mu saboda kai dan Najeriya ne na gaskiya kuma jari ga Jihar Kaduna. Mun yi imani ba don irin gwagwarmayarku ba da har yanzu kasar nan muna cikin mulkin kama-karya.”
Sanata Shehu Sani ya kara da cewa tsohon Gwamnan wanda shi ne shugaban Jam’iyyar PRP yana daya daga cikin ’yan Najeriya da suka rika sukar lamarin mulkin soja a lokacin da mafi yawan manyan ’yan Nejariya suka yi shiru saboda tsoro.
Ya ce saboda yawan sukar da Balarabe Musa ke yi wa mulkin sojoji ne ya sa aka rika kama shi amma duk da haka bai daina ba.
Sanata Shehu Sani ya ce ba zai taba yarda da duk wani tsari ko doka da wata gwamnati a kasar nan za ta fitar ko yi don matsa wa talakawa ba. Ya ce Talakawa ne suka zabe su saboda haka ba zai taba yarda a takura musu ba.
A jawabin Alhaji Balarabe Musa yaba wa Sanata Shehu Sani ya yi da ya samu damar kai masa ziyara har gida, inda ya kwatanta shi da mutum mai kaunar talakawa.
“Sanata Shehu Sani ya dade yana ba mu goyon baya a gwagwarmayar da muke yi a kasar nan duk da cewa jam’iyyarmu ba daya ba. Na san shi sama da shekara 35 kuma dukkanmu muna da ra’ayin ci gaban kasar nan ne kawai da na talaka,” inji shi.
Alhaji Balarabe Musa ya ce a shirye yake ya hada hannu da Sanata Shehu domin kawo sauki ga rayuwar talaka da kuma ci gaban Najeriya.