’Yan sumoga sun kasayar da kullin kwayoyi 119 a filin jirgin Abuja
Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke aiki a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe Abuja sun bayyana kama wasu mutane uku da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi, inda biyu daga cikinsu suka kasayar da kullin miyagun kwayoyi guda 119 daga duburarsu. Babban jami’in kula da ma’aikatan na NDLEA a Abuja, […]

Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke aiki a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe Abuja sun bayyana kama wasu mutane uku da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi, inda biyu daga cikinsu suka kasayar da kullin miyagun kwayoyi guda 119 daga duburarsu.
Babban jami’in kula da ma’aikatan na NDLEA a Abuja, Jonah Acheme ya bayyana cewa, wadanda aka kama, John Prince Louis Ifechukwu da bictor Chibuzor Olochukwu Anadu da kuma Omotayo Anifowoshe, an kama su ne a kofar fita daga wurin tantance matafiya a filin jirgin.
Ya ce Ifechukwu, dan shekara 31 ya shigo jirgi ne daga Legas, aka kama shi a filin jirgin Abuja, inda yake shirin shiga wani jirgin domin zuwa birnin Jakarta na kasar Indonesiya. “Ifechukwu, wanda dan kasuwa ne da ke sayar da suturun mata a Kasuwar Balogun da ke Legas, ya kasayar da kulli 65 na wasu kwayoyi masu nauyin giram 864,” inji shi.
Ya ce an kama shi ne da bizar izinin halartar baje koli a kasar Indonesiya da kuma tikitin jirgin sama na kamfanin zirga-zirga na Ethiopia, inda ya yi ikirarin cewa zai tafi birnin Jakarta ne domin sayo suturun mata. Ya ce wani abokinsa ne ya shirya masa wannan tafiya kuma ya hada shi da wani mutum da bai san shi ba, wanda shi ne ya ba shi wadannan kulle-kullen magunguna domin ya kai masa su zuwa kasar Indonesiya.
“Shi kuwa Anadu, wanda magidanci ne, dan asalin garin Oraifite ne, kusa da Ozobullu, jihar Anambra. An kama shi ne a yayin da yake kokarin tafiya kasar Indonesiya. Ya kasayar da kulli 54 na kwayoyin, masu nauyin kilogiram 1,073,4” inji jami’in NDLEA Acheme.
Ya bayyana cewa shi kuwa wanda ake zargi na uku, Anifowoshe, ’yar shekara 37, ’yar asalin Epe Jihar Legas ne. An kama ta ne a lokacin da ta sauka Abuja daga Legas, tana shirin tafiya Afrika ta Kudu. An kama ta ne saboda ta yi kokarin tsallake shingen masu bincike a filin jirgin na Abuja.
“An kama ta ne tana dauke da manyan jakunkuna biyu dauke da kwayoyin Ephedrine mai nauyin kilogiram 3 da kuma hodar koken mai nauyin kilogiram 1.9. magungunan na boye ne a wasu boyayyun aljifan jakunkunan biyu. Matar ta amsa cewa farkanta ne ya ba ta jakunkunan kuma shi ne ya aike ta da su.”
Kwamandan NDLEA a filin jirgin Abuja, Hamisu Lawan ya bukaci da a sanya na’urorin fallasa kwayoyi a filin, sannan kuma ya koka da yadda aka hade wuraren binciken fasinjojin fita waje da kuma na cikin gida.