’Yan ta’adda ba za su yi nasara a Najeriya ba

Mummunan ta’addanci da kiyayya sun kai makura wajen salwantar da rayukan ’yan Najeriya, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. A Nyanya, motar da aka dana wa bom ta halaka mutum 72. Wasu daruruwa sun ji munanan raunuka. Wadannan kashe-kashe ba su da wata manufa da ta wuce daukaka miyagun ayyuka. Rugugin fashewa […]

’Yan ta’adda ba za su yi nasara a Najeriya ba
’Yan ta’adda ba za su yi nasara a Najeriya ba

Mummunan ta’addanci da kiyayya sun kai makura wajen salwantar da rayukan ’yan Najeriya, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. A Nyanya, motar da aka dana wa bom ta halaka mutum 72. Wasu daruruwa sun ji munanan raunuka. Wadannan kashe-kashe ba su da wata manufa da ta wuce daukaka miyagun ayyuka. Rugugin fashewa bom ya zama tamkar mugun barawo, wanda za mu dade ba mu daina jin zafin mummunan illar da ya yi ba na tsawon lokaci.
Asarar da kasar nan ta yi ba a iya mayar da makwafinta. Wadannan adadi na mutane  72 na nuni da wasu alkaluma kashe-kashen da aka saba jinsu. Sai dai al’amarin da ya auku ya fi gaban abin da ake zato. Dole mu mike wajen shawo kan wannan matsala, tun kafin miyagu su yunkura wajen kai mu inda suke nufi.
Bai kamata mu kyale dilalen mutuwa su karya mana lago, mu afka cikin mummunan tarkonsu ba. Wadanda aka kashe ba kawai wani adadi ba ne da aka rubuta a shafuka. Su mutane ne, wadanda ke da nama da jini a jiki da ruhi tamkar kowa a cikinmu. Akwai wadanda suka kasance iyaye maza da mata na wadansu, ko ’yan uwa da ’yar uwa. Suna da iyaye; sun kuma kasance ’ya’yan wadansu. Su magidanta ne ko matan aure da suka yi makwaftakar aminci da abokan hulda. Suna da burin rayuwa. Sun kasance abin kauna, kuma sun nuna kaunarsu ga wadansu. A halin yanzu rayuwarsu ta tafi, wadanda suka damu da su dole ne su yi ta jimami da alhinin da aka  tursasa su yinsa.
Wadannan mutane ba su da wani laifi. Laifinsu kawai sun kasance masu fafutikar neman abincinsu, don kula da kawunansu da iyalansu. Saboda wannan kawai aka kashe su.
Su jigo ne a wakilan masu ayyukan neman abin gudanar da rayuwa. Mafi yawansu ba sa rayuwa cikin jin dadi. Mafi yawansu suna aikin wahala mai daukar dogon lokaci, sannan su karbi albashin da bai taka kara ya karya ba. Sukan yi asubanci a kowace safiya, don fafutikar neman abincinsu. Suna fama da matsalolin zamantakewa da kalubalen da ke tattare da arziki da sauran matsalolin da suka dabaibaye al’umma, amma duk da haka aikinsu suke yi, ba sa cutarwa, manufarsu kawai ita ce kyautata rayuwar iyalansu da makusantansu (majibantansu).
Wadannan mutane rayuwarsu a kange take, haka ma mutuwarsu ta kasance. Har yanzu ma ba mu san sunayensu ba. A da suna tare da mu. Suna da hankoron buri irin namu. Muna kokarin kyautata rayuwar ’ya’yanmu, tare da samar musu kyakkyawar makomar rayuwa. Muna son rayuwa cikin kima da mutumtaka. Muna son zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da makwaftanmu ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ko tushe ba. Muna neman yalwar arziki don kauce wa talauci. Muna bukatar ’yan uwantaka don kauce wa tashe-tashen hankula. Muna bukatar zaman lumana, tare da kin rugugin bama-bamai.
A wannan karon, ba mutum 72 kawai aka cutar a harin ba. Kowane daya daga cikinmu ya yi asarar wani abu a wannan ranar. Duk wannan asarar da wahalar da aka yi fama da ita, bai kamata mu lullube cikin tsoro ba, har ta kai mu ga kyale masu tallata hajar mutuwa su ci nasara a kanmu ba.
Wadanda suka aikata wannan aiki, sun daura yaki kan duk wani abu managarci da inganci. Ba wai a kan kasa ko gwamnati suka daura yaki ba. Sun daura yaki da  Najeria da daukacin al’ummar Najeriya, saboda wannan kisan gilla ya dauki rayukan maza da mata, tsofaffi da matasa, kiristoci da Musulmi. A yunkurin da ake yi na tsoratarwa da firgitarwa da raba kawunanmu, su kansu miyagu na yi wa kawunansu illa. Don sun nuna mana cewa sai sun wahalar da mu ta irin wannan mummunan zalunci.
Ba tare da la’akari da addininmu ko garin haihuwarmu ba, duk an zubar jinanenmu, an kuma raunata mu ta irin wannan hanyar zalunci. Tausayawa na nan a cikin koyarwar kowane addini da kabilun da suka hadu suka haifar da mutanen Najeriya.
Muna da bambance-bambancenmu, amma mafi yawan ’yan Najeriya kansu a hade yake wajen adawa da mummunan tashin hankalin da aka yi a Nyanya da sauran wurare.
Irin wannan aika-aika ba ta da wurin zama a Najeriya.  Don haka wadanda ke yin ta’asa ba su da wurin zama a kasarmu. Masu aikata miyagun ayyuka sun yi kama da mutane. Ta yiwu suna da gabobin jiki da fuskoki irin namu, amma su ba irinmu ba ne. A dabi’arsu ta kisan gilla ga mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, sun zama azzalumai. Sun yi hannun riga da tsarin tausaya wa dan Adam. Uwarsu ita ce zubar da jini, kuma ubansu shi ne zalunci. Sun kaddamar da yaki a kan al’ummar Najeriya. Sun yi nuni da cewa ba so suke yi sun ’yantar da mutane ba. Bukatarsu, su hallaka su. Duk da karfin mugun nufinsu da makauniyar kiyayyarsu, za su gaza. Mutanen Najeriya masu kyakkyawar manufa za su yi nasara.
Irin wannan mugun nufin ba zai kai ga nasara ba. Mun yi nisa wajen tafiyar da kasar nan, mun jajirce wajen hakuri kan al’amura da dama, don haka ba za mu yarda wadannan miyagun masu aika-aika su kawar da hankalinmu ba.
Wadannan miyagu masu tallata hajar mutuwa, ba su tsaya kan yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, kisan gilla, har ma sun kai ga sace ’yan mata fiye da 100 a makarantarsu. Mene ne dalilin satar mata ’yan makaranta? Kowace irin manufa suka kudura, to su shirya tunkarar fushin ’yan Najeriya. Dole su sako wadanan ’yan mata ba tare da sun cutar da su ba. Aikata sabanin haka zai tabbatar da sun aikata mumunan laifi, abin ki.
Dole ne mu farga a daidai wannan lokaci don tunkarar babban kalubalen da ke gabanmu. Wasu ’yan tsirari na kokarin durkusar da kasar nan, ta hanyar ta’addanci. Don haka, dole ne mu hada kai , mu dage wajen tunkararsu. Bai kamata mu kyale miyagun laifukan da suka tafka su tafi sakaka ba, mu hada kai wajen tabbatar da ganin an hukunta su.
Ina kira ga gwamnati ta ja damara, ta sake shiri, bisa la’akari da kara yaduwar irin wadannan miyagun ayyuka. Don a bayyane yake karara, akwai bukatar a kara inganta dabarun tattara bayanan sirri, a ingantasu ta yadda za a karya lagon makircin ’yan ta’adda kafin su aiwatar da muguwar manufarsu. Sannan akwai bukatar a fito da shirye-shiryen kyautata zamantakewa da bunkasa tattalin arziki  a sassan kasar nan da ake fama da wadannan matsaloli, don jawo hankalin al’umma. A samar wa matasa mafita, ta yadda masu mummunar manufa ba za su yaudare su ba. A yi hanzarin bullo da tsarin cimma manufa nan take, da ta dogon zango wajen samar da ayyukan yi.
Tabbas Najeriya za ta samu nasarar shawo kan matsalar, amma al’amarin ba zai yiwu ba, ana zaune sakaka kawai ba. Akwai bukatar managartan dubaru.
Ni a kashin kaina da jam’iyyata, mun yi tur da Allah wadai da wadannan hare-hare da ma wasunsu. Don haka wadanda suke aikata aika-aikar, za su fahimci cewa kowace kusurwa ta kasar nan na adawa da mummunan aikinsu.
Duk da cewa muna hamayyar siyasa da jam’iyya mai mulki, bai kamata mu sanya siyasa a kan al’amuran da ke da matukar muhimmanci ga dorewar kasarmu da kyautatuwar zaman lafiyarta ba.
Mun dauki alkawarin kare hadin kan kasar nan, kuma ba za mu aikata wani abu da zai gurgunta harkokin tsaron kasa ba. Ba ma bukatar samu wani fifiko ko daukakar siyasa a cikin wannan musifa, don haka muke yi wa gwamnati mai ci fatan samun nasara a yakin da take yi.
A shirye muke da mu taimaka ta hanyar da tadace don yin wannan yaki da mummunan aiki. Za mu hada karfi da kyakkyawar manufa kan wannan al’amari.
Najeriya da ’yan Najeriya sun sha matukar shan wahala. Wadanda ke mulkin kasar nan a halin yanzu da wadanda za su mulketa a nan gaba, dole su kawar da bambance-bambancen siyasarsu, ta yadda za su lalubo hanyoyin da za mu hada kai wajen kare wannan kasar, tare da cikakken tsaro ga kowa.
Ina godiya a gareku tare da fatan Allah Ya albarkaci al’ummar Tarayyar Najeriya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno