’Yan ta’adda na bata sunan Musulunci – Sardaunan Katsina
Tsohon Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim Kumasi, Sardaunan Katsina, ya zargi kungiyoyin ’yan ta’adda da yin amfani da addinin Musulunci ta hanyar da ba ta dace ba, suna kashe jama’a a nahiyoyi daban-daban na duniya. Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron da kungiyar ASALLIN ta shirya […]
Tsohon Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim Kumasi, Sardaunan Katsina, ya zargi kungiyoyin ’yan ta’adda da yin amfani da addinin Musulunci ta hanyar da ba ta dace ba, suna kashe jama’a a nahiyoyi daban-daban na duniya.
Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron da kungiyar ASALLIN ta shirya a Abuja a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, kungiyar Boko Haram suna yin amfani da addini bisa kuskure, suna janyo tashin hankali a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Ya kara da cewa haka ma kungiyar ’yan ta’adda ta Alka’ida da ISIS su ma sun yi amfani da addini suna tayar da hanakulan jama’a a Nahiyar Afirka ta Arewa da kuma gabas ta tsakiya.
Ya ci gaba da cewa ba su tsaya a kan tayar da hankula ba har wureren tarihi da ke kasashe daban-daban suka ruguza.
“A cikin shekaru shida da suka gabata babu bala’in da ’yan Najeriya suka gani da ya kai na ’yan kungiyar Boko Haram. Makarantar Arabiya da ke garin Ngala da ke jihar Borno tana daya daga cikin wureren da ’yan Boko Haram suka kai wa hari. Wannan bai tsaya a Najeriya ba kawai hatta kungiyoyin Alka’ida da ISIS su ma sun tayar da tarzoma da kashe-kashe da kuma ruguza wuraren tarihi.” Inji shi.
Ya zargi ’yan ta’adda da yin amfani fa harshen Larabci suna bata addinin Musulunci.
Ya bayyana cewa ’yan ta’adda suna amfani da harshen Larabci idan za su aika da faifan bidiyo. Hakan inji shi yana sanya wa wadanda ba su jin harshen su zaci Larabci yana da alaka da ta’addanci.