’Yan ta’adda sun dasa bom a makarantu da asibitocin Kaduna

’Yan ta’adda na yunkurin cutar da al’umma ta hanyar dasa ababen fashewa a makanrantu, asibitoci, gidajen abinci da wuraren ibada da sauransu

’Yan ta’adda sun dasa bom a makarantu da asibitocin Kaduna

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai

Gwamanatin Kaduna ta gargadi al’ummar jihar da su yi hattara saboda ’yan ta’adda sun dasa ababen fashewa a asibitoci da makararantu da sauran wuraren taron jama’a a jihar.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gidan ta Jihar Kaduna, ta ce ta gano haka ne bayan bayanan sirri da ta tattaro bayan binciken da hukumomin tsaron jihar suka gudanar.

Kwamishina mai kula da ma’aiktar, Samuel Aruwan, ya sanar a ranar Litinin cewa, “’Yan ta’adda na yunkurin cutar da al’umma ta hanyar dasa ababen fashewa a makanrantu, asibitoci, gidajen abinci, wuraren ibada, manyan hanyoyi, otal-otal, wuraren shakatawa, da wuraren casu.”

Amma ya ce hukumomin tsaro ka’in da na’in domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da na gwamnatin.

Ya kuma sanar da lambobin kar-ta-kwana da jama’a za su kira a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su yarda da shi ba: 09034000060 da kuma 081701899990.

Sanarwar tasa na zuwa ne washegarin tashin wani abun fashewa a wani kangon otal da ke unguwar Kabala a garin Kaduna, duk da cewa ba a samu asarar rai ba.

Aruwan ya shawarci mutanen Kaduna da su kasance masu lura da duk wani motsi ko kayan da ba su aminta da su ba, musamman a muhimman wurare da yankunansu.

Ya kuma bukace su da su rika duba harabar wuraren da suke zaune a-kai-a-kai tare da sanar da hukumomi idan suka ga wani abin da ba su yarda da shi.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma shawarci masu sanar fasa duwatsu da su tabbatar da tsaron kayan aikinsu, domin kar su fada a hannun masu mugun nufi.

A cewarta, za ta rika gudanar da zagaye a wuraren fasa duwatsu domin tabbatar da bin wannan umarni.

Bugu da kari, za ta ci gaba da bin duk matakan da suka dace na tabbatar da tsaron al’umma.