’Yan ta’adda na kashe Musulmi da sunan jihadi – Muftin Saudiyya
Babban Muftin Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al-Asheikh, wanda har wa yau shi ne Shugaban Majalisar Manyan Malaman kasar ya gargadi matasa su guji jirkita ma’anar jihadi wajen aikata barna a kasashen Musulmi suna kashe fararen hula haka kawai da sunan Musulunci.Al-Asheikh ya kuma bukaci matasan su guji ruduwa da farfagandar irin wadancan kungiyoyin ’yan ta’adda.“Muna […]
Babban Muftin Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al-Asheikh, wanda har wa yau shi ne Shugaban Majalisar Manyan Malaman kasar ya gargadi matasa su guji jirkita ma’anar jihadi wajen aikata barna a kasashen Musulmi suna kashe fararen hula haka kawai da sunan Musulunci.
Al-Asheikh ya kuma bukaci matasan su guji ruduwa da farfagandar irin wadancan kungiyoyin ’yan ta’adda.
“Muna ci gaba da ganin miyagun ayyuka a kafafen talabijin da makiya Musulunci ke aikatawa. Wadannan miyagun kungiyoyi suna ta zubar da jinni ba tare da dalili ba, suna kashe ’yan uwa Musulmi da sunan Musulunci, alhali abin da suke yi ba komai ba ne, face shiryayyen ta’addanci da sata. Kuma wadannan miyagun mutane suna fakewa da sunan jihadi wajen aikata ta’asarsu,” inji Al-Asheikh.
Ya kara da cewa, “Zama cikin lumana da kwanciyar hankali abu ne da ya zama tilas kuma haka addini ya bukaci a yi. Kashe fararen hula haka kawai ba ma yana bata sunan Musulunci kawai ba ne, har ma yana jefa iyalan wadanda aka kashe danginsu a cikin babban bala’i.”
Ya ce, dokokin Musulunci sun haramta zubar da jini kuma sun karfafa mabiyansa su sauke nauyin amanar da aka halicce su dominta.
Al-Asheikh ya nanata yadda Alkur’ani Mai girma da Sunnar Annabi (SAW) suka nuna haramcin kashe rai haka kawai. “Alkur’ani ya nuna cewa: “Duk wanda ya kashe mumini da gangan sakamakonsa Jahannama ne yana mai dauwama a cikinta,” inji shi.
Al-Asheikh ya bukaci Musulmi su rika karanta ayoyi da hadisan da suka yi magana kan martabar rai inda ya nanata bukatar su dakatar da wannan kisan rashin imani.
Ya tunatar da Musulmi cewa Ubangiji bai son kashe koda mushirikai ne bisa zalunci, kuma Manzon Allah (SAW) ya sanya kisan kai cikin manyan kaba’ira bakwai masu halakarwa.